Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)

Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)

-Allah yayi wa matar Sheikh Ibrahim Nyass dake karin Okene rasuwa

- Wasu rahotanni sun yi nuni da cewar Sayyada Bilkisu ta dade da rabuwa da Shehin malamin

Tsohuwar matar fitaccen malamin darikar Tijjaniyya, wato Sheikh Ibrahim Nyass, Bilkisu Okene ta rasu a ranar Lahadi 16 ga watan Afrilu a garin Okene.

KU KARANTA: Karshen duniya! Wata yarinya ta kashe kanta saboda son da take yiwa malamin ta

A ranar Litinin 17 ga watan Afrilu ne aka yi mata jana’iza inda aka binneta a garin na Kogi, sai dai da fari anyi cece kuce tsakanin yan uwanta aka kodai a kai ta can kasar Sanigal ne?

Don a binne ta a daidai inda aka binne tsohon mijinta, shehin malami Nyass.

Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)
Sheikh Ibrahim Nyass tare da Sayyada Bilkisu

Legit.ng ta kawo muku wasu daga cikin hotunan jana’izar Sayyada Bilkisu.

Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)
Gawar matar Sheikh Ibrahim Nyass data rasu a jihar Kogi

Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)
Jana'izar matar Sheikh Ibrahim Nyass

Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)
Matar Sheikh Ibrahim Nyass, Sayyada Bilkisu

Allah ya jikanta, Amin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda direban wani babban faston Najeriya ya musulunta

Asali: Legit.ng

Online view pixel