Yabon gwani ya zama dole; shugaba Buhari na kokari sosai – Inji wani tsohon gwamna

Yabon gwani ya zama dole; shugaba Buhari na kokari sosai – Inji wani tsohon gwamna

- Tsohon gwamnan jihar Abiya, Dokta Orji Uzor Kalu ya yaba wa shugabancin shugaba Muhammadu Buhari

- Kalu ya shawarci ‘yan Najeriya cewa a tallafa wa gwamnatin shugaba Buhari da kuma daina sukar shugaban

- Tsohon gwamnan ya bukaci shugaban kasa da ya daidaita tsakanin jihohin kasar musanmma yankin Kudu maso gabas da kuma Kudu maso Kudu

Tsohon gwamnan jihar Abiya, Dokta Orji Uzor Kalu, ya yi kira ga 'yan Nijeriya, don tallafa wa gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari da kuma daina sukar shugaban.

Kalu ya ce a halin yanzu shugaba Buhari na kokari, domin haka yana bukatar goyon bayan kowane dan Najeriya.

Jigon dan siyasar, ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu a gidan Cif Goddy Imo a Ohafia, jihar Abiya. Inji NAIJ.COM.

Yabon gwani ya zama dole; shugaba Buhari na kokari sosai – Inji wani tsohon gwamna

Tsohon gwamnan jihar Abiya, Dokta Orji Uzor Kalu a wata gangamin jam'iyyar APC

Wadanda suke amfani da rashin lafiyar shugaban kasa, don yada jita-jita sun kasace jahilai saboda kowa na iya rashin lafiya. Shugaban ya yi rawar gani, musamman a fannin tsaro.

Ya ce: "’Yan Najeriya ba su tambayar abu mai yawa daga shugaban, suna bukatar abinci, lafiya da kuma tsaro da sauran muhimman bukatu.”

KU KARANTA KUMA: An sake bude filin jirgin sama na Abuja, Buhari ya cika alkawari

Tsohon gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya da daidai tsakanin jihohin kasar musanmma yankin Kudu maso gabas da kuma Kudu maso Kudu a tsakanin sauran jihohi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon da wani dan jam'iyyar APC ke bayyana nadamar kasancewa a cikin jam'iyyar saboda masaloli daban-daban da ta ke fuskanta a hannun 'yan jam'iyyar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel