Yan bindiga sun sace dan kasuwa a jihar Niger

Yan bindiga sun sace dan kasuwa a jihar Niger

- Wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sunyi garkuwa da wani dan kasuwa

- Sun nemi a biya kudin fansa naira miliyan daya

- Shugaban hukumar NSCDC na jihar Niger yace hukumar ta fara aiki don ceto dan kasuwan a raye

Yan bindiga takwas sun sace wani dan kasuwa, Alhaji Nuhu Isa a ranar Lahadi, a kauyen Lambata dake karamar hukumar Gurara na jihar Niger.

Shugaban hukumar NSCDC na jihar, Mista Philip Ayuba, ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna a ranar Talata, 18 ga watan Afrilu.

Ayuba ya ce tuni yan bindigan sunyi amfani da wayar wanda abun ya shafa don kiran yan’uwansa sannan kuma sun nemi a biya naira miliyan daya a matsayin kudin fansa.

Yan bindiga sun sace dan kasuwa a jihar Niger

Yan bindiga sun sace dan kasuwa a jihar Niger

Ya ce masu garkuwan sun zo ne dauke da muggan makamai tare da harbi a kauyen kafin su sace dan kasuwan.

KU KARANTA KUMA: Kalli kywawan hotunan sabuwar matar Ahmed Musa guda 8

Ya ce tuni hukumar ta fara aiki don ceto dan kasuwan a raye.

“Mun hada kai da sauran hukumomin tsaro don ceto ran dan kasuwan,” cewar shugaban hukumar.

Ya yi kira ga al’umman kananan hukumomi na Gurara, Suleja da kuma Paikoro da su bayar da bayanai masu amfani da zai iya taimakawa gurin ceto wanda abun ya shafa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yaya zaku ji idan shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kawo karshen Boko Haram?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel