Ya kamata Buhari ya yi murabus yanzu – Asu Beks

Ya kamata Buhari ya yi murabus yanzu – Asu Beks

- Shugaban kungiyar Ijaw Peoples Assembly (IPA), Elder Asu Beks ya bayar da dalilin da zai sa buhari yin murabus a yanzu

- Ya ce Buhari ya mayar da hankali ga lafiyar sa

- Ya kuma shawarci shugaban kasar da karda ya bari na kewaye da shi su basa gurguwan shawara

Shugaban kungiyar Ijaw Peoples Assembly (IPA) da kuma kungiyar Ijaw Media Forum (IMF), Elder Asu Beks ya bayar da dalilin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus a yanzu.

Jaridar Sun ta ruwaito cewa Beks ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari baya cikin cikakken lafiya a yanzu sannan kuma don haka ya yi murabus domin ya mayar da hankali ga lafiyar sa.

NAIJ.com ta tattaro cewa ya yi ikirarin cewa wadanda ke kewaye da fadar shugaban kasa na ba shugaban kasa gurguwar shawara.

Ya kamata Buhari ya yi murabus yanzu – Asu Bek

Asu Beks ya shawarci shugaba Buhari da ya mayar da hankali ga lafiyar sa

Ya ce: “Shugaban kasa ya sauke kafafunsa kasa, shine shugaban jam’iyyar, shine shugaban kasar sannan kuma ya sauke kafafunsa saboda abunda na sani shine na kewaye da shugaban kasa ne ke basa gurguwar shawara.

KU KARANTA KUMA: Kalli kywawan hotunan sabuwar matar Ahmed Musa guda 8

“Sannan kuma yin magana game da wadannan na kewayen, wadannan mutanen basu fi hudu zuwa biyar ba, wadanda ke ba shugaban kasa gurguwan shawara sannan kuma da zafi-zafi a kan bugi karfe don haka ya yi gaggawan basu umurni, domin hakan zai fiye mana gaba daya."

Ya kara da cewa idan akayi la’akari da matsayin lafiyar Buhari a wannan lokaci, ya kamata ya yi murabus kamar yadda a yanzu ba ya da karfin da zai fuskanci zafin gwamnati.

Ya kara da cewa: “Ina ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya cikin koshin lafiya.

“Da ace ni ne shi zan mayar da hankali ga lafiya na ne. akwai wata sanarwa kwanaki na cewa zai tafi birnin Landan don ci gaba da ganin likita.

“Sanarwan kamar shiru ne ga lokacin da zai tafi hutu. Ina ganin lafiya ba abu bane da mutun zai yi wasa da shi. Dole sai shugaban kasa Muhammadu Buhari yana raye sannan zai iya shugabantar kasar, matattu basa mulki.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani mutumi da ya nemi a kakkabe majalisar dattawa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel