Ra’ayi : Ni matsalata da mai martaba bata da yawa indai ya warware rudanin da ya cusa min a kaina

Ra’ayi : Ni matsalata da mai martaba bata da yawa indai ya warware rudanin da ya cusa min a kaina

Wani marubuci yayi wasu bayanai game mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu akan wasu maganganu da yayi. Ku sani cewa dukkan abinda ke kunshe cikin wannan rubutu ra’ayin marubucin ne ban a jaridar NAIJ.com ba.

Daga :- Ibrahim Umar Bari.

Wani marubuci yayi wasu bayanai game mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu akan wasu maganganu da yayi. Ku sani cewa dukkan abinda ke kunshe cikin wannan rubutu ra’ayin marubucin ne ban a jaridar NAIJ.com ba,

1. A baya Kwankwaso ya hana bara kai kuma kace bai isa ba sai anyi bara a kano, yau kuma kai ne da kan ka kake yaki da bara me yasa haka?

2. A baya mutanen Danbatta sun yi dokar aure kace basu isa ba, yau kuma kazo ka na kafa taka dokar auren kuma wai doka ce dole kowa sai yabi, saboda me?

3. Kana da hanyar jawo hankalin shuwagabanni ba tare da kowa ya ji ba amma kullum kana media kana sukar su, wannan daidai ne?

KU KARANTA: Mota ta buge mutane 2

4. Kace dole yarinya sai ta kai shekara sha takwas za'ayi mata aure amma baka ce mana kada ta haura shekaru kaza ba'ayi mata aure ba, ko meyasa?

5. Kace idan miji ya mari matarshi ta rama, to ranka ya dade idan mata ta mari miji fa?

6. 'yan mata musamman na kano sun ciri tuta wajen karatun addini, yarinya karama ka ganta tayi sauka, shin meyasa kullum mai martaba baka yabo saidai fito da jahilcin su?

Shin karatun addini ba karatu bane?

Me martaba wallahi mu masu kaunar ka ne kuma kullum addu'ar fatan alkhairi muke yi maka amma ba dole sai mun yiwa addinin mu da al'adun mu kwaskwarima don kawai a kira mu wayayyu ba.

Allah yaja zamanin sarki.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel