Ali Ndume ya sami kasaitacciyar tarba a Borno ta Kudu

Ali Ndume ya sami kasaitacciyar tarba a Borno ta Kudu

- Sanata Ali Ndume ya samu kasaitacciyar tarba daga mutanen yankin Borno ta Kudu

- Ndume ya shaida wa magoya bayansa ainihin dalilan da ya sa aka dakatar dashi a majalisar

- Sarakunan Biu da Shani sun tabbatar wa Sanata Ali Ndude goyon bayansu dari bisa dari sannna sun jinjina masa akan kyawawan ayyukan da yake yi wa mazabunsa

Sanata mai wakiltan Borno ta kudu ya samu kasaitacciyar tarba daga mutanen yankin Borno ta Kudu da yake wakilta.

Al'umman mazabar da Sanata Ali Ndume ke wakilta na ci gaba da jinjina goyon bayan su ga sanatan duk kuwa da dunbin kalubale da ya ke fuskanta a majalisa.

A baya NAIJ.com ta ruwaito inda sanata Ali Ndume ya shaida wa dandazun magoya bayan sa a jihar cewa ba zai roki shugaban majalisar ba ko wai don a dawo dashi saboda a iya sanin sa bai aikata wani laifin da zai sa a dakatar dashi ba.

“Ina so in sanar mu ku cewa na yi matukar farin cikin wannan tarba da akayi mini. Duk da cewa an nemi da in rubuta wasika ga shugaban majalisar akan ya hakura a dawo dani majalisar, na ki yin haka saboda ni har yanzu ban ga laifin da nayi ba da za’a ce wai in je in roki wani. An nemi da in sasanta da su na ce babu abin da zan sasanta akai saboda ban aikata laifi ga kowa ba."

Ali Ndume ya sami kasaitacciyar tarba a Borno ta Kudu

Ali Ndume ya sami kasaitacciyar tarba daga al'umman mazabar sa

Ndume ya shaida wa magoya bayansa ainihin dalilan da ya sa aka dakatar dashi a majalisar.

KU KARANTA KUMA: Fasto da yaransa biyu sun musulunta, sun aske gashin su (HOTUNA)

“Na fara samun matsalane tun bayan nuna goyon bayana ga kudirorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake aiko wa majalisa. Sannan Kuma da kokarin ganin cewa majalisar ta amince da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC.

"Na tsaya tsayin daka a matsayina na shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai. Hakan bai yi ma wasu dadi ba.

“Shugaban Majalisar yana da ikon ya dakatar da ni a lokacin da na tashi a majalisar domin gabatar da korafi na, amma da ya ke suna da wata shiri da ba ni da masaniya akai sai ya bari domin suci mutunci na."

Sarakunan Biu da Shani sun tabbatar wa Sanata Ali Ndude goyon bayansu dari bisa dari sannna sun jinjina masa akan kyawawan ayyukan da yake yi wa mazabunsa.

KU KARANTA KUMA: Kalli kywawan hotunan sabuwar matar Ahmed Musa guda 8

A abaya NAIJ.com ta rahoto cewa majalisar dattijai ta dakatar da Ali Ndume har na tsawon kwanaki 181 saboda kama shi da tayi yana bada bayanan karya akan wasu ‘ya’yan majalisar da ya hada da shugaban majalisar, Bukola Saraki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mutumi yayi barazanar yin sata idan abubuwa basu daidaita ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel