Yadda ake shigo da shinkafa a boye cikin kasar nan

Yadda ake shigo da shinkafa a boye cikin kasar nan

– Wani tsohon Jami’in Gwamnati ya bayyana cewa ana shigo shinkafa a boye

– Gwamnati dai ta haramta shigo da shinkafa cikin kasar

– Sai dai wasu bata-gari suna yi ba daidai ba

Yadda ake shigo da shinkafa a boye cikin kasar nan

Wasu na tsallako da shinkafa a boye

Wani tsohon Darekta a Ma’aikatar yada labarai na Najeriya ya rubuta wasika ga shugaban kwastam na kasa Hameed Ali inda yake bayyana masa cewa wasu na cigaba da shigo da shinkafa a boye cikin kasar.

NAIJ.com ta samu labari cewa Peter Dama ya bayyana cewa an shigo da sama da motoci 100 cike da shinkafa ta iyakokin kasar ta kasar Kano da Katsina da sauran su da sa-hannun wasu bata-gari har a cikin Jami’an kwastam din.

KU KARANTA: An sallami Ma'aikatan NNPC da aka samu da laifi

Yadda ake shigo da shinkafa a boye cikin kasar nan

Shugaba Buhari ya dage wajen harkar noman shinkafa a kasa

Idan har aka cigaba da fasa kaurin dai yunkurin wannan Gwamnati na noma shinkafar da kasar za ta ci na fuskantar barazana. Gwamnatin shugaba Buhari ta dage wajen harkar noma a kasar domin Najeriya ta rika ciyar da kan ta.

Masu nazari kuma sun bayyana cewa barayin kasar ne dai suka yi sanadiyyar tashin farashin Dala a kasar. Haka Hukumar NBS ta kasa tana cewa farashin kaya sun fara yin kasa a Najeriya. Farashin kaya sun sauka kasa da kashi 0.52% yanzu haka.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

yanayin farashin kaya lokacin hutun nan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel