Yadda mutanen Buhari ke sata a Najeriya-Inji Gwamna Fayose

Yadda mutanen Buhari ke sata a Najeriya-Inji Gwamna Fayose

– Gwamnan Ekiti ya kara dura kan shugaba Buhari

– Ayo Fayose yace na-kusa da Buhari na buga sata a Abuja

– Gwamna Fayose yace doka ba ta aiki kan ‘Yan APC

Yadda mutanen Buhari ke sata a Najeriya-Inji Fayose

Fayose ya ce mutanen Buhari na sata a Villa

Yayin da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta CAN ta ke yabawa kokarin Gwamnatin Najeriya wajen yaki da ta’addancin Boko Haram. Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti ya soki Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnan yace na-kusa da shugaban kasa Buhari musamman wadanda suka kashe kudin wajen yakin neman zabe suna cin karen-su-ba-babbaka a cikin a Fadar Aso Villa. Fayose yace irin wadannan mutane suna can su na sata a cikin fadar shugaban kasar.

KU KARANTA: Kungiyar SERAP ta budawa Buhari wuta

Yadda mutanen Buhari ke sata a Najeriya-Inji Fayose

Mutanen Buhari na sata a Najeriya-Inji Gwamna Fayose

Fayose ya maida martani ne ga Ministan yada labarai Lai Mohammed da ya bayyana cewa har a makabartu Jama’a sun koma boye kudin da su ka sace. Shi dai Fayose yace yakin da ake yi da ‘Yan PDP ne kurum ban da na-kusa da shugaban kasar.

Dama NAIJ.com ta kawo maku cewa shi dai Gwamna Ayo Fayose yana da ja game da kudin da aka gano kwanaki a Legas inda har ya zubawa shugaba Buhari tambayoyi rututu. Gwamnan yace dai akwai sauran rina a kaba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dubi inda Gwamna Fayose ya koma

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel