Kiristocin Borno sun yabawa Gwamnatin Buhari

Kiristocin Borno sun yabawa Gwamnatin Buhari

– Yan Kungiyar CAN sun ce sun ga canji da zuwan shugaban kasa Buhari

– CAN ta Jihar Borno ta yabawa Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari

– Kwanan nan ne Kiristoci suka yi bikin ‘Easter’

Kiristocin Borno sun yabawa Gwamnatin Buhari

Boko Haram: An yabawa Gwamnatin Buhari

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya watau CAN ta yabawa kokarin Sojojin Najeriya masu yaki da ta’addancin Boko Haram. CAN din ta jinjinawa irin kokarin da Sojojin kasar suka yi wajen fada da ‘Yan Boko Haram.

NAIJ.com na da labari cewa Kiristocin Jihar Borno sun bayyana cewa bana sun yi bukukuwan ‘Easter’ da aka saba cikin kwanciyar hankali. Kiristocin Borno suka ce an dade rabon da su samu kwanciyar hankali irin wannan karo.

KU KARANTA: 'Yan Chibok sun soki shugaba Buhari

Kiristocin Borno sun yabawa Gwamnatin Buhari

CAN ta Jihar Borno ta yabawa Sojojin Najeriya

Bishof Mohammed Naga wanda shi ne shugaban Kungiyar Kiristoci watau CAN yayi wannan bayani a wani taro da aka yi. Bana dai an yi bikin ‘Easter’ ba tare da wani takunkumi ko fitinar Boko Haram ba a Jihar Borno.

Su kuma ‘Yan Kungiyar BBOG watau BringBackOurGirls sun bayyana cewa shugaba Buhari ya ba da kunya inda ya gaza ceto ‘yan matan na Chibok da aka sace tun Afrilun 2014. Shugabannin Kungiyar Aisha Yesufu da Oby Ezekwesili suka bayyana wannan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Dan Biyafara ya buga baram-barama

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel