An zargi bankuna da jami’an kwastam da satar dala $30 tiriliyan a cikin shekara 11

An zargi bankuna da jami’an kwastam da satar dala $30 tiriliyan a cikin shekara 11

- An zargi bankuna da jami’an kwastan na Najeriya tare da jami’an bankuna da laifin wawure tsabar kudi na kimanin Dala tiriliyan 30 tsakanin 2006 zuwa 2017

- Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da hukumar kwastan da kudaden shiga daga hukumar ne ya bayyana haka a jiya

Sanata Hope Ozodinma, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gano yadda aka wawure kudaden da kuma samo hanyar da za a toshe kafafen da ake bi ana sace kudaden, ya ce za su yi iya kokarin su domin tabbatar da cewa sun cika umarnin da majalisa ta ba su domin ganowa da kuma dinke bakin zaren.

NAIJ.com ta tsinkaye shi yana cewa: “Idan ba ku manta ba, an ba mu umarnin gano hanyoyin da aka wawure kudaden da kuma samo duk wasu hanyoyin da za a toshe yadda ake satar kudaden shiga na kasar nan daga harajin kayan da ake shigowa da su daga kasashen waje.

“Kwamitin mu ya fara bincike, kuma mun samu nasarar gano wasu hanyoyi da ake karkatar da kudaden harajin da ake karba.

''Mun kuma samu damar shiga cikin rumbun ajiyar bayanai na kwamfutocin Hukumar Kwastan, inda muka gano yadda ake yin asarkala da kudaden musaya na kasashen waje.”

An zargi bankuna da jami’an kwastam da satar dala $30 tiriliyan a cikin shekara 11

An zargi bankuna da jami’an kwastam da satar dala $30 tiriliyan a cikin shekara 11

Wannan rumbun adana bayanai, kamar yadda sanatan ya bayyana, “cike ya ke da muna-muna sosai. Muna fa magana ne a kan kudade zunzurutu har Dala Tiriliyan 30, kuma duk mun mika bayanan da muka samo ga bankunan da suka sai wa masu shigo da kaya daga kasashen waje kudaden musaya.”

KU KARANTA: Zan wadata kasar nan idan Buhari ya bani dama - Obasanjo

Ya kara da cewa sun yi taron ganawa da wadannan bankuna, inda suka ba su wa’adin makonni uku domin su yi nazarin takardun bayanan, su kawo musu hujjojin cewa an yi amfani da kudaden.

Ya ci gaba da cewa wannan harkalla ta kawo karancin kudaden musaya na kasashen waje a cikin Najeriya, alhali kuma babu wasu hujjojin da ke nuna cewa an shigo da kayyaki daga kasashen waje da kudaden.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wasu jami'an gwamnati ne ke amsa tambayoyi a kotu saboda almundahana

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel