Jama’a ba su amince da wani nadin shugaba Buhari ba

Jama’a ba su amince da wani nadin shugaba Buhari ba

– Mutanen Yankin Basawa sun ce ba su amince da nadin Gwamnatin tarayya ba

– Jama’ar Basawa sun yi tir da nadin Farfesa Barminas a matsayin shugaban NARICT

– An koka cewa ba a bi doka wajen nadin shugaban cibiyar

Jama’a ba su amince da wani nadin shugaba Buhari ba

Ba a amince da sabon shugaban cibiyar NARICT ba

Jama’ar Yankin Basawa da Samaru ba su yi amanna da sabon nadin da shugaban kasa Buhari yayi ba a cibiyar bincike da nazari na NARICT. Hassan Umaru da Kasimu Balarabe su ka rubuta wasikar korafi ga shugaban kasar inda su ka nuna cewa ba su amince ba.

Jama’ar yankin suka ce ba a bi dokar da ta dace ba wajen nadin sabon shugaban cibiyar binciken ba. A ka’ida ya kamata a tallata kujerar a jarida kafin ayi nadin sai dai wannan karo ba ayi haka ba. Mutanen yankin suka ce ya kamata a yi gaskiya wajen nadin.

KU KARANTA: Buhari ya nada Jelani Aliyu shugaban Hukumar kera motoci

Jama’a ba su amince da wani nadin shugaba Buhari ba

Shuganan rikon kwarya na NARICT

Tuni dai wa’adin shugaban cibiyar nazarin Farfesa Idris M. Bugaje ya cika har aka nada Farfesa Mohammed Kabir Yakubu rikon kwarya. Sai dai yanzu shugaba Buhari ya nada Farfesa Jef T Barminas a matsayin sabon shugaban cibiyar.

Jama’a ba su amince da wani nadin shugaba Buhari ba

Farfesa Idris Muhammad Bugaje

Haka NAIJ.com ta kawo maku labarin Jelani Aliyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada ya jagoranci Hukumar NADDC ta kasa mai kula da sha’anin kere-keren motocin zamani. Yanzu haka ana jira Jelani ya kawo sauyi na tsare-tsare a sha’anin kirar motoci a kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Babbar magana: Ka ji abin da wani dan Biyafara yake fada

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel