Ba zan ba Saraki hakuri ba don ya maida ni – Inji Ali Ndume

Ba zan ba Saraki hakuri ba don ya maida ni – Inji Ali Ndume

- Sanata mai wakiltan Barno ta Kudu yace ba zai roki shugaban Majalisar dattijai ba saboda wai a dawo dashi zauren Majalisa.

- Ali Ndume yace har yanzu bai iya gano laifin da yayi ba da majalisar ta dakatar dashi.

Ndume ya shaida wa magoya bayansa ainihin dalilan da ya sa aka dakatar dashi daga zauren majalisar a taron gangami da jama’ar mazabunsa su ka yi domin tarbar sa a ziyarar da ya kai gida.

NAIJ.com ta samu labarin cewa yace: “Na fara samun matsala ne tun bayan nuna goyon bayana ga kudirorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake aiko wa majalisa.''

Sannan Kuma da kokarin ganin cewa majalisar ta amince da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC.

Na tsaya tsayin daka a matsayina na shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai. Hakan bai yi ma wasu dadi ba.

Ba zan ba Saraki hakuri ba don ya maida ni – Inji Ali Ndume

Ba zan ba Saraki hakuri ba don ya maida ni – Inji Ali Ndume

Shugaban Majalisar yana da ikon ya dakatar da ni a lokacin da na tashi a majalisar domin gabatar da korafi na, amma da yak e suna da wata shiri da ba ni da masaniya akai sai ya bari domin suci mutunci na.

KU KARANTA: Zan kamo Jonathan da Diazani - Magu

Sarakunan Biu da Shani sun tabbatar wa Sanata Ali Ndude goyon bayansu dari bias dari sannna sun jinjina masa akan kyawawan ayyukan da yake yi wa mazabunsa.

“Ko kana majalisa ko baka majalisa muna bayan ka a yankin Barno ta Kudu.“

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Wani jigon jam'iyyar APC yace za'a kori jam'iyyar a zabe mai zuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel