Da kyau: Darajar dala za ta zazzago wannan makon

Da kyau: Darajar dala za ta zazzago wannan makon

– A wannan makon Dala za tayi kasa a Najeriya

– Shugaban ‘Yan canji na kasa ya bayyana wannan

– Dalar ta daga sama bayan a baya ta sauka

Da kyau: Darajar dala za ta zazzago wannan makon

Gwamnan CBN na kasa Emifiele

Kasar Najeriya na fama da durkushewar tattalin arziki tun bara bayan ragargajewar farashin man fetur. Sai dai kasar na murmurewa bayan da alkaluma suka nuna cewa har tsadar kaya na kara sauki a cikin kasar.

Shugaban ‘Yan canji watau Bureau De Change 'BDC' Alhaji Aminu Gwadabe ya bayyana cewa dalar za ta sauko wannan makon. Babban bankin kasar na CBN na cigaba da sakin makudan daloli domin darajar dalar ta sauko kasa.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta maidawa wani Lauya martani

Da kyau: Darajar dala za ta zazzago wannan makon

Shugaban kasa Buhari da Mataimakin sa da Legarde ts IMF da Gwamnan CBN

A wancan makon dalar har ta kai N403 sai dai Alhaji Gwadabe yace yana sa rai wannan makon za tayi kasa da haka. Ana dai shirin daidaita farashin da ake da su na kudin kasar wajen tsakanin kasuwa da banki.

Masu nazari dai sun bayyana cewa barayin kasar ne dai suka yi sanadiyyar tashin farashin Dalar a kasar. NAIJ.com na da labari daga Hukumar tara bincike da alkaluman kasa watau NBS cewa farashin kaya sun fara yin kasa a Najeriya. Farashin kaya sun sauka kasa da kashi 0.52%

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kaya na kara tsada a kasuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel