Ba wanda ya jefe ni a taron APC na Funtua - Inji Senata Abu Ibrahim

Ba wanda ya jefe ni a taron APC na Funtua - Inji Senata Abu Ibrahim

- Sanata Abu Ibrahim dake wakiltar shiyar Funtua a majalissar dattawan Nijeriya, ya musanta zargezargen cewa an jefe shi a gangamin taron shiyar APC da aka gunadar ranar Asabar a garin Funtua

- Sanatan ya ce wadanda suka tada hayaniyar yan jam'iyyun adawa ne da aka dakko hayarsu domin tada hargitsi, wajen amsar yan jam'iyyar PDP da suka dawo APC, domin ganin taron bai yi nasara ba

Jaridar NAIJ.com ta samu labarin cewa a hirarsa da manema labarai jiya a Kaduna, ya bayyana cewa yana zargin wadanda suka sha kayi a jam'iyyar PDP, ne suka haddasa wannan rikicin.

A yanzun ina gab da cike shekara 70, ba abin da zai ja man daukar yan bangar siyasa, na fito zabe har sau hudu a jam'iyyar adawa kuma ina lashe zabe, ba tare da yan ta'adda ko murdiyar zabe ba.

Mun fito takara tare da su, sun sha kasa, kuma sun san cewa madamar ina cikin siyasa, ba za su taba cin nasarar zabe ba, amma ba mamaki wannan ne zai iya sa su kai man hari." Inji Abu Ibrahim din.

Ya kara da cewa wadanda suka tada hayaniyar ba matasan Funtua bane, an dai dakko hayarsu ne daga wajen jihar Katsina domin a yi amfani da su wajen tada husuma.

"Kamar kullum kowane taron siyasa sai an sami mutane masu nuna goyon bayansu ga wanda suke marawa baya, suna daga hotunansa, tare kuma da kushe ga abokin karawaru, dole kuma ka sami masu nuna maka soyayya ko akasin haka, wanna kuma sha'ani ne na siyasa.

Senata Abu Ibrahim

Senata Abu Ibrahim

"An kirani na yi jawabi na, na kuma gabatar da shi, tun a nan na gane akwai matsala, na hangi wani mutum da bai kamata a ce yana cikin taron ba, tare da mabiya wadanda ba kimtsattsu ba, wanda ya canza sheka daga PDP zuwa jam'iyyarmu, amma ya ci gaba da yin bangar siyasa kamar yadda ya sani can a jam'iyyar PDP, inji shi.

Bayan na gama jawabi na, gwamna ya hau yana yin nasa, wani ya zo ya gaya man cewa akwai matsala, wasu na neman tada hayaniya da cin mutunci.

KU KARANTA: Za'a gina kasuwar zamani a garin Funtua

"Kamin a kira mu zuwa jawabin rufe taro wasu suka fara jifa da duwatsu, wannan ne ya sa aka yanke hukuncin cewa na bi tawagar gwamna mu fita, amma na ki, sai muka fice tare da Sanatan shiyar Katsina ta tsakiya Umar Kurfi muka yi gida. Amma na fara karanta labaru a kafafen sadarwa na zamani, cewa wai an man kofar raggo kuma an buge ni.

"Amma ku kanku shaida ne ina cikin koshin lafiya, ba wanda ya jefe ni ko duka na, motocina kuma suna nan ba wanda ya fasa su.'' Inji Sanata Abu Ibrahim a Kaduna.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ku wani matashi ne ke yiwa jam'iyyar Sanatan kaca kaca

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel