John Terry zai bar Chelsea bayan buga wasanni 713

John Terry zai bar Chelsea bayan buga wasanni 713

- Jagorar teburin gasar Firimiya, Chelsea, ta ba da sanarwar cewar Keftin dinta, John Terry, zai bar kungiyar a karshen kakar bana.

- Terry, mai shekara 36 da yake buga baya ta tsakiya, ya buga wa Chelsea wasanni 713 tun da ya fara taka mata leda a shekarar 1998, kuma sha mata kwallaye 66.

Ya kansace keftin din Chelsea a wasanni 578 - adadin da babu wanda ya taba yi - amma a kakar bana ya fara wa kungiyar wasanni hudu ne kawai a gasar Firimiya.

NAIJ.com ta tsinkaye shi yana cewa: "Ina jin ina da gudumawa mai yawa da zan iya bayarwa a kan fili, amman na fahimta cewar damar da zan iya samu a Cheslea ba ta da yawa."

A wani labarin kuma, Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce suna fuskantar "babban kalubale" wajen cancantar shiga gasar cin kofin Zakarun Turai, yana mai cewa babu abin dsa ya sauyawa game da makomarsa a kungiyar.

John Terry

John Terry

Kashin da Crystal Palace ta bai wa Arsenal da ci 3-0 ranar Litinin ya mayar da kungiyar a matsayi na shida, inda take bayan Manchester City, wacce ke matsayi na hudu, da maki hudu koda yake tana da ragowar wasanni takwas.

KU KARANTA: Arsenal na fuskantar babban kalubale - Wenger

Wenger, wanda kwantaraginsa zai kare a lokacin bazarar da ke tafe, ya jagoranci Arsenal zuwa matsayi na hudun farko a teburin gasar a dukkan kakar wasa 20 da suka buga.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli yadda karawa tsakanin Najeriya da Senegal zata kasance

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel