Sojojin Najeria sun ceto mutum 1,623 daga Boko Haram

Sojojin Najeria sun ceto mutum 1,623 daga Boko Haram

- Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta bisa hadin gwiwar 'yan sintiri sun ceto mutane 1,623 daga hannun 'yan Boko Haram

- Sojojin sun fatattaki 'yan kungiyar ta’addan Boko Haram daga Jarawa a jihar Borno

- Anyi wa kananan yaran da aka ceto allurer rigakafi

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta bisa hadin gwiwar 'yan sintiri sun ceto mutane 1,623 daga hannun 'yan Boko Haram, bayan sun fatattaki 'yan kungiyar a jihar Borno.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar, ta ce sojojin sun yi aiki ne da wani bayanin sirri na maboyar 'yan kungiyar a yankin Jarawa ta karamar hukumar Kala Balge.

Sanarwar ta ce sojojin suna shiga kauyen na Jarawa sai aka bude musu wuta, a inda sojojin suka mayar da martani.

Sojojin Najeria sun ceto mutum 1,623 daga Boko Haram

Sojojin Najeria sun ceto mutum 1,623 daga Boko Haram

Daga nan ne kuma sojojin suka shiga kauyukan Deima da Artano da Saduguma da Duve da Bardo da Kala da Bok da Msherde da kuma Ahirde, domin fatattakar 'yan kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Fasto da yaransa biyu sun musulunta, sun aske gashin su (HOTUNA)

Sanarwar ta ce sojojin sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 21, baya ga ceto mutanen 1,623 da suka hada da mata da kananan yara.

NAIJ.com ta kawo cewa yanzu haka dai kamar yadda sanarwar ta ce, tuni aka kwashi mutanen 1,623 zuwa sansanin 'yan gudun hijra da ke Rann, bayan an diga wa kananan yara allurar rigakafi.

Kalli sauran hotunan a kasa:

Sojojin Najeria sun ceto mutum 1,623 daga Boko Haram

Anyi wa yara allurar rigakafi

Sojojin Najeria sun ceto mutum 1,623 daga Boko Haram

Tuni aka kwashi mutanen 1,623 zuwa sansanin 'yan gudun hijra da ke Rann

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon sojojin Najeriya da suka fatattaki yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel