Zan wadata kasar nan in har Shugaba Buhari ya bani dama - Obasanjo

Zan wadata kasar nan in har Shugaba Buhari ya bani dama - Obasanjo

- Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya shawarci jihohi da kuma gwamnatin tarayya da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yake jagoranta da su haɗa hannu da manoma a yunƙurin kawar da yunwa kafin shekara ta 2025.

- Obasanjo yayi wannan kiran ne a gidansa dake Abeokuta babban birnin jihar Ogun, lokacin da ƴan ƙungiyar haɗakar manoma ta Egba suka kai masa ziyarar ban girma.

Obasanjo ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban wata ƙungiya da ake kira ‘Zero Hunger Farmers Organisation in Nigeria’ a turance yace sun ƙudiri aniyar kawar da yunwa ta hanyar ƙara samar da abinci ta yadda zai zamanto babu wani ɗan Najeriya da zai kwanta da yunwa.

NAIJ.com ta samu labarin cea Yace idan da za a basu goyon baya da kuma ƙarfafa musu gwiwa manoma zasu samar da abinci wadatacce kuma mai sauƙin farashi, wanda hakan zai haifar da wadatar abinci a cikin ƙasa.

Obasanjo

Obasanjo

A tabakin Obasanjo “gwamnati zata iya taimakon manoman dake ƙasarnan ta hanyar tsare-tsare da kuma samar da yanayi mai kyau da zai haifar da samar da abinci”.

KU KARANTA: An budowa Buhari wuta game da wannan matsalar (Karanta)

Tsohon shugaban ƙasar ya shwarci manoman da sufara haɗakar noman: Kifi, kaji, rogo da kuma shinkafa kafin su shiga noman samar da ƴaƴan itatuwa wanda yace hakan yana ɗaukan lokaci kafin afara cin amfaninsu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wani jigon APC ke bayyana yadda zasu sha kasa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel