Tsoron jifa ya fara hana Sanatocin Arewa zuwa mazabun su

Tsoron jifa ya fara hana Sanatocin Arewa zuwa mazabun su

- Al'ummar jihar Bauchi, sun bayyana cewa tsoron jifa ya hana Sanatocin su zuwa Bauchi tun bayan jifan da akayiwa sanata Ali wakili da sanata Isah Hamma Misau.

- Sanatocin wadanda su ka ci zabe, a karkashin jam'iyyar APC. Amma daga bisani suka yi butulci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Barista Muhammad Abdullahi Abubakar.

Gami da watsi ga talakawan jihar Saboda wasu bukatunsu wanda bana talakawan jahar ta Bauchi ba.

"A dalilin haka yanzu sanatocin suka, shirya wata makarkashiya domin kawo rudani a fadin jihar. Wanda ta haka su ke son samun damar shiga cikin jihar ta Bauchi domin gujewa fushin talakawa.

Yanzu haka dai sun dauki hayar wasu matasa su kimanin 200 domin jifan mai girma gwamnan Barista Muhammad Abdullahi Abubakar" a wajen taro kamar yadda wani matashi wanda ya nemi a sakaya sunansa kuma yana cikin wandanda aka bawa wannan kwangilar ya bayyana.

Tsoron jifa ya fara hana Sanatocin Arewa zuwa mazabun su

Tsoron jifa ya fara hana Sanatocin Arewa zuwa mazabun su

NAIJ.com ta tattaro cewar Dama dai an dade ana zargin sanatocin jihar ta Bauchi da yunkurin kawo rikici a fadin jihar, da kuma kauda hankalin mutane daga ayyukan Alkhairi da mai girma gwamnan M.A Abubakar ya ke yi a fadin jihar.

KU KARANTA: Tambayoyi 10 da Fayose yayi Buhari

Binciken da wasu yan jarida su ka yi ya nuna cewa jihar Bauchi bata taba samun gwamna mai hankali da nutsuwa da kishin jihar ba kamar M.A Abubakar wanda cikin shekaru biyu kurrum ya canja fasalin jihar ta Bauchi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kuna goyon bayan a rushe majalisar dattijai? Ga ra'ayin wasu yan Najeriya nan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel