YANZU-YANZU: An sake kai wani gagarumin hari a wani kauye a kudancin Kaduna

YANZU-YANZU: An sake kai wani gagarumin hari a wani kauye a kudancin Kaduna

- Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi suka da kakkausar murya kan harin da aka kai kauyen Asso dake kudancin Kaduna.

- El-Rufai ya mika Jajen sa ne ga mutanen kauyen da aka kai ma wannan mummunar hari a wata sanarwa da kakakin gwamna Samuel Aruwan ya sanya wa hannu.

Bayan haka kuma ya sanar da kafa wata sabuwar rundunar jami’an soji da akayi wa suna ”Operation Harbin Kananan” kuma zata fara aiki a yankin kudancin Kaduna na ba da dadewa ba.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ba a sanar da yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar harin ba.

Rikici irin wannan ya sha faruwa a yankin kudancin Kaduna inda bayanai da suka fito a wancan lokacin ya nuna cewa akalla mutane 200 ne suka rasa rayukansu a ire-iren wadannan hare-hare.

kudancin Kaduna

kudancin Kaduna

KU KARANTA: Karatun Boko zai zama kyauta a wannan jihar (Karanta)

El-Rufai ya ce gwannati zata yi duk abin da ya kamata domin ganin an fatattaki irin wadannan ‘yan ta’adda a dazukan yankin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wani rikicin ne da ya faru a Kudancin Kaduna dina

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel