Tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya yabawa Gwamnatin Buhari

Tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya yabawa Gwamnatin Buhari

- Tshohon Gwamnan Kano kuma tsohon ministan Ilimi a Najeriya Malam Ibrahim Shekarau ya bayayyana cewa yaki da cin hanci da rashawa a wannan Gwamnatin ta Buhari abun a yaba mawa ne.

- Tsohon Gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillacin labarai na Najeriya a garin Sokoto a yan Litinin.

Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito Shekarau din yana cewa: "Tabbas kokarin da shugaba Buhari keyi wajen yaki da cin hanci da rashawa yana da kyau sosai."

NAIJ.com ta ruwaito cewa tsohon ministan ya kuma ce: "Kamata yayi a anshe dukiyar duk wanda ya sameta ba ta halastacciyar hanya ba." Ya kara da cewa lokacin da yake Gwamnan Kano a cikin shekara ta 2005 ya kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa a jihar.

Sai dai kuma jigon a jam'iyyar PDP ya kuma ce dole ne a yi yakin ba tare da son kai ba.

Tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau

Tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau

A wani labarin kuma, Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, Ibrahim Magu, ya ce.

Hukumata ba za-ta daga kafa ga duk wanda taci karo da shi ba, matukar binciken hukumar ya kai ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, babu shakka zan kamo shi.

KU KARANTA: Babu wani yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya - Fayose

Kuma yanzu haka ina kokarin ganin cewa na dawo da tsohuwar ministar man fetur ta kasa Misis Alison Maduke, gida domin ta fuskanci shari'a abin mamaki kusan rabin satar da aka tafka a kasar nan duk a ofishinta ta faru, saboda haka batun yaki da cin hanci da rashawa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wasu jami'an Gwamnati ne a Kotu da ake tuhuma da cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel