Abubuwan da mutane ke fada game da yaki da sata na Gwamnatin Buhari

Abubuwan da mutane ke fada game da yaki da sata na Gwamnatin Buhari

– Gwamnatin Buhari ta shirya yaki da sata a Najeriya

– Wasu na ganin su kurum aka shirya kai wa hari

– Yayin da wasu ‘Yan kasar ke ganin hakan yayi daidai

Abubuwan da mutane ke fada game da yaki da sata na Gwamnatin Buhari

Gwamnatin Buhari ta shirya yaki da rashin gaskiya

Yayin da wannan Gwamnatin mai-ci ta shugaba Muhammadu Buhari ta ke yakar sata a Najeriya, Jama’a na da ra’ayi mabambanta game da yakin. Inda wasu musamman 'yan adawa ke ganin su ake hari wasu kuma na ganin fa laifin su ne ya jawo masu.

Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti yace babu wani yaki da sata da ake yi a kasar nan. NAIJ.com ta kawo maku rahoto a baya ma cewa Gwamnan yana da ja inda har ya zubawa shugaban kasa Buhari tambayoyi game da wasu kudi da aka gano kwanaki yace da wala-kin.

KU KARANTA: Yaki da rashin gaskiya: Fayose ya soki Buhari

Abubuwan da mutane ke fada game da yaki da sata na Gwamnatin Buhari

Shugaban kasa Buhari tare da Ibrahim Magu na EFCC

Wani babban Lauya a kasar Mike Ozekhome yayi tur da yaki da satar da wannan Gwamnati ta faro yace asali ma batawa kasar suna ake yi. Fadar shugaban kasar dai tayi kaca-kaca da wannan magana. Dama can dai fadar tace wannan yaki ba na shugaba Buhari kadai ba ne.

Shi kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Ministan Ilmi a da Malam Ibrahim Shekaru yace aikin shugaban kasar na kyau. Ibrahim Shekarau yace duk wanda ya saci kudin Najeriya a damke sa kurum.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Dan APC ya gargadi 'Yan Jam'iyyar ta su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan
NAIJ.com
Mailfire view pixel