Jose Mourinho ya dauki fansa a kan Chelsea

Jose Mourinho ya dauki fansa a kan Chelsea

– Man Utd ta ba Chelsea kashi a Gasar Firimiya

– Kungiyar Manchester ta ba doke Chelsea da ci 2-0

– Chelsea sune a kan saman teburin Gasar

Jose Mourinho ya dauki fansa a kan Chelsea

Man Utd ta ba Chelsea kashi 2-0

NAIJ.com na da labari a bangaren wasanni cewa Kungiyar Manchester United ta ba Chelsea kashi a Gasar Firimiya ta Ingila. Man Utd din dai ta doke Chelsea ne da ci 2 da nema ta hannun Dan wasa Rashford da kuma Ander Herrera.

Chelsea ce dai ke saman teburin Gasar na Firimiya amma kuma hakan ya sa ta rage maki inda Tottenham ke jiran ko-ta-kwana. Kocin Chelsea Conte yace sun yi sakaci a wasan kuma ya dauki laifi.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa Dan wasa Ahmed Musa ya rabu da matar sa

Jose Mourinho ya dauki fansa a kan Chelsea

Man Utd ta dauki fansa a kan Chelsea

A farkon kakar bana dai Chelsea ta dagargaza Man Utd a Filin Stamford Bridge da ci 4-0. Wannan karo tsohon Kocin Chelsea Jose Mourinho ya dauki fansa. Tun da Koci Mourinho yake wasa a Ingila dai babu kulob din da ta taba dukan sa gida-da-waje.

Barcelona da Real Madrid sun yi nasara a Kasar Spain da ci 3-2 inda Isco da Lionel Messi suka jefawa Kungiyar su kwallaye biyu. A kasar Italiya kuma kunnen doki aka yi tsakanin Inter Milan da AC Milan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Super Eagles na Najeriya suna shirin wasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel