Gwamna Tambuwal ya yabawa Majalisar Dokoki

Gwamna Tambuwal ya yabawa Majalisar Dokoki

– Gwamna Aminu Tambuwal ya yabawa Majalisar Jihar sa

– An kawo kudirin da zai wajabta sa yara a Makarantar Boko

– Har wa yau ilmin Boko zai zama kyauta a Sokoto

Gwamna Tambuwal ya yabawa Majalisar Dokoki

Gwamna Tambuwal na Sokoto

NAIJ.com na samun labari cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yaba da kokarin Majalisar dokokin Jihar Sokoto da ta tabbatar da kudirin karatun kananan yara a Jihar. Wannan kudiri zai ba yara damar karatu kyauta.

Kudirin da ta zama doka za ta ba yara ‘yan shekaru 6 har zuwa 18 damar karatun Boko kyauta a fadin Jihar. Sannan kuma ya zama dole iyaye su tura ‘Ya ‘yan su Makaranta wanda har za a iya hukunta wadanda suka saba wannan doka.

KU KARANTA: ‘Yan Kungiyar BringBackOurGirls sun soki Buhari

Gwamna Tambuwal ya yabawa Majalisar Dokoki

Wata Malamar makaranta a Najeriya

Gwamna Tambuwal ya yabawa ‘Yan Majalisar da wannan kokari ta bakin Mista Imam Imam. Sai dai wani yana ce mana ba girin-girin ba tayi mai don kuwa wasu lokuta iyakar dokar cikin takardar da aka rubuta su.

Kwanakin baya wata Kungiya mai suna YouthHubAfrica tayi wani taro domin ganin kawo karshen matsalolin Almajiranci da rashin zuwa makaranta musamman a Yankin Arewa irin su Jihar Sokoto.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An sace 'Yan mata daga Makaranta yau shekaru 3

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel