Barayin gwamnati sun fara binne kudaden da suka sata a makabartu – Lai Muhammad

Barayin gwamnati sun fara binne kudaden da suka sata a makabartu – Lai Muhammad

- Ministan yada labarai Lai Muhammad ya ce rahotanni da gwamnati ke samu na nuna cewa wasu daga cikin wadanda suka wawushe kudaden kasa suna binne su

- Ya ce shirin bayar da lada ga wadanda suka tona asirin barayin gwamnati ya haifar da da mai ido

- Ministan ya yaba wa ‘yan Najeriya game da hadin kai da suka baiwa shirin

- Ya kara da cewa gwamnati za ta baiwa ‘yan Najeriya cikakken rahoto akan adadin kudaden da aka samu da zaran an kammala komai

Ministan yada labarai Lai Muhammad ya ce rahotanni da gwamnati ke samu na nuna cewa wasu daga cikin wadanda suka wawushe kudaden kasa a yanzu haka sun fara binne su a makabartu, da jeji da bayan gidajen su.

Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu ta hannun mai bashi shawara na musamman Segun Adeyemi.

Ya ce shirin bayar da lada ga wadanda suka tona asirin barayin gwamnati ya haifar da da mai ido, inda a yanzu haka hukumar EFCC ta gano makudan kudade ta hanyar sa.

Barayin gwamnati sun fara binne kudaden da suka sata a makabartu – Lai Muhammad

Ministan bayanai da al'adu, Alhaji Lai Muhammad

Ministan ya yaba wa ‘yan Najeriya game da hadin kai da suka baiwa shirin. Ya ce yawancin masu tona asirin su na yin haka ne saboda kishin kasa ba saboda kudin da za su samu ba.

KU KARANTA KUMA: Senata Abu Ibrahim ya sha da kyar bayan jama’ar mazaɓarsa sun kai masa hari (BIDIYO)

NAIJ.com ta rahoto inda ministan ya kara da cewa da zaran an warware rikice rikicen da suke tattare da wasu daga cikin kudaden, an kuma kammamala shari’ar da ake yi akan wasu, toh gwamnati za ta baiwa ‘yan Najeriya cikakken rahoto akan adadin kudaden da aka samu.

A karshe, ya jaddadawa masu tonan asirin cewa gwamnati za ta ba su kariya tare da biyan su cikakken kason su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mai goyon bayan Biafra yace shi Allah ne.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel