Fayose ya zubawa shugaba Buhari tambayoyi 10 masu zafi

Fayose ya zubawa shugaba Buhari tambayoyi 10 masu zafi

– Gwamna Ayo Fayose ya aikawa shugaban kasa Buhari wasu tambayoyi

– Tambayoyin dai game ne da kudin da Hukumar EFCC ta gano kwanan nan

– Gwamnan yace akwai abin da Gwamnatin APC ke boyewa

Fayose ya zubawa shugaba Buhari tambayoyi 10 masu zafi

Fayose ya makawa shugaba Buhari wasu tambayoyi

NAIJ.com ta kawo maku labarin cewa Gwamnan Jihar Ribas yace makudan kudin da Hukumar EFCC ta gano a wani gida a Ikoyi kwanan nan na Jihar sa ne tun lokacin tsohon Gwamna Rotimi Amaechi wanda yanzu Ministan Buhari ne.

Ana dai nema a jefa Amaechi cikin matsala duk da kuwa ya musanta haka kuma Hukumar NIA na tsaro tana bayyana cewa kudin ta ne. Sai dai Gwamna Fayose na Jihar Ekiti yana da ja inda ya zubawa shugaba Buhari tambayoyi. Kadan daga ciki:

KU KARANTA: Buhari ya jagwalgwala kasar nan-Tanko Yakassai

Fayose ya zubawa shugaba Buhari tambayoyi 10 masu zafi

Gwamna Ayodele Fayose na Ekiti

1. Kudin wanene EFCC ta gano?

2. A cikin gidan wa aka samu kudin?

3. Idan har gidan na Hukumar NIA ne yaushe aka saye gidan kuma wa ya kama haya?

4. Ya aka yi aka samu labarin cewa akwai kudi a cikin gidan?

5. Ta ya aka yi NIA take gudanar da wani aiki shugaban kasa bai da labari?

Dsr.

Shi dai Gwamna Fayose yana da ja yana ganin akwai sauran rina a kaba yana cewa APC na boye wani abu. Dama Kungiyar SERAP tace ya kamata shugaban kasar ya fitar da Jama’a daga cikin duhu a daina boye-boye kowa ya gane wanda ya mallaki wadannan kudi

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mutumi ya kai kukan sa ga Gwamnati

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel