Kungiyar SERAP ta bazowa shugaban kasa Buhari wuta

Kungiyar SERAP ta bazowa shugaban kasa Buhari wuta

– Kungiyar SERAP ta nemi shugaban kasa Buhari yayi ma jama’a bayani

– Kwanan nan Hukumar EFCC ta gano wasu makudan kudi

– Har yanzu dai ana ta kai kawo game da maganar kudin

Kungiyar SERAP ta bazowa shugaban kasa Buhari wuta

Shugaban Kungiyar SERAP

Kungiyar SERAP ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bayani ga ‘Yan Najeriya game da makudan kudin da Hukumar EFCC ta gano a Ikoyi kwanan nan. Kungiyar tace ya kamata shugaba Buhari ya fadawa Duniya ko wa ya mallaki kudin.

NAIJ.com ta kawo maku rahoton cewa Kotu ta bada umarni a mikawa Gwamnatin tarayyar Najeriya makudan kudin da Hukumar EFCC ta bankado bayan an rasa masu shi. Wata majiyar tace shugaban kasa ya bada umarni a maidawa bankin kasar kudin.

KU KARANTA: Kungiyar BBOG sun caccaki shugaba Buhari

Kungiyar SERAP ta bazowa shugaban kasa Buhari wuta

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu

Gwamnan Jihar Ribas yace kudin Jihar sa ne tun lokacin tsohon Gwamna Rotimi Amaechi wanda ya zama Ministan Buhari. Sai dai kuma Hukumar NIA na tsaro tana bayyana cewa kudin ta ne ita mana wani aiki da aka shirya tun lokacin shugaba Jonathan.

Adetokunbo Mumuni na SERAP yace ya kamata shugaban kasar ya fitar da Jama’a daga cikin duhu a daina boye-boye kowa ya gane wanda ya mallaki wadannan kudi. Kungiyar SERAP tace dole a rika bayani gar-da-gar ba tare da wani nuku-nuku ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jama'a na shan wahala wajen rajistar jarrabawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel