Za a cire shingayen karbar haraji a titunan Najeriya

Za a cire shingayen karbar haraji a titunan Najeriya

- Rundunar Yan sandan Najeriya zata fara cire shinge da aka sanya ba bisa ka’ida ba a kan manyan hanyoyin mota

- Shingayen sun hada da wadanda hukumomin karban haraji ke sanya wa ba bisa ka'ida ba

- Rundunar tace zata kama duk wani mutun ko kungiya da aka samu ta na karbar haraji a hannun masu motoci a kan manyan hanyoyi

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce daga ranar Litinin, jami'anta na musanman za su fara cire duk wani shinge da aka sanya ba bisa ka'ida ba a kan manyan hanyoyin mota a fadin kasar.

Shingayen sun hada da wadanda hukumomin karban haraji ke sanya wa ba bisa ka'ida ba, da na kungiyoyin masu motocin sufuri da na kungiyoyin kwadigo, wadanda suke kawo cikas ga zirga-zirgar jama'a da kaya a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Senata Abu Ibrahim ya sha da kyar bayan jama’ar mazaɓarsa sun kai masa hari (BIDIYO)

Cikin wata sanarwa, rundunar 'yan sandan ta ce jami'an ta za su kuma kama duk wani mutun ko kungiya da aka samu ta na karbar haraji a hannun masu motoci a kan manyan hanyoyi.

Za a cire shingayen karbar haraji a titunan Najeriya

Sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris

NAIJ.com ta samu labarin cewa rundunar 'yan sandan ta ce dokar karban kudin haraji a kasar ta haramtawa hukumomi ko wani mutun sanya shinge a kan manyan hanyoyi da nufin karbar haraji.

KU KARANTA KUMA: Ni kai na ba ni da lafiya ina ga Buhari-Gwamna El-Rufai

Acewar rundunar 'yan sandan, bayanan da ta samu daga korafe-korafen jama'a sun nuna a lokuta da dama, bata gari, na amfani da ire-iren shingayen wajen aikata laifuka, da suka hada da garkuwa da mutane da fashi da makami.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Me zai sa ka iya kashe kan ka?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel