Shugaba Buhari yayi sakaci Inji ‘Yan BringBackOurGirls

Shugaba Buhari yayi sakaci Inji ‘Yan BringBackOurGirls

– Yan Kungiyar nan ta BBOG sun soki shugaban kasa Buhari

– ‘Yan BBOG din suka ce shugaba Buhari yayi sakaci

– Har yanzu da dama cikin ‘Yan matan Chibok ba su dawo gida ba

‘Yan Kungiyar BBOG sun soki shugaba Buhari

Wasu daga cikin 'Yan matan Chibok da aka sace

A baya NAIJ.com ta kawo maku rahotanni game da cika shekaru 3 da aka yi da sace ‘Yan matan nan na Chibok. Har yau dai da yawa ba su dawo gida ba ko da yake wannan Gwamnati tayi nasara wajen ceto dubunnan ‘Yan mata da yara daga hannun Boko Haram.

‘Yan Kungiyar BBOG watau BringBackOurGirls sun bayyana cewa shugaba Buhari ya ba da kunya inda ya gaza ceto ‘yan matan na Chibok da aka sace tun Afrilun 2014. Shugabannin Kungiyar Aisha Yesufu da Oby Ezekwesili suka bayyana wannan.

KU KARANTA: An fara gano fuskokin 'Yan Boko Haram

‘Yan Kungiyar BBOG sun soki shugaba Buhari

Aisha Yesufu ta Kungiyar BBOG

Kungiyar suka ce duk wata nasara da aka samu idan har ba a gano yaran Garin Chibok ba ba ayi komai ba. ‘Yan BBOG suka ce sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba don haka dole a tashi tsaye. Shugaban kasa Buhari dai yace ba su daina iya bakin kokarin sub a.

‘Yan Kungiyar na BringBackOurGirls masu kokarin ganin ‘yan matan Chibok da aka sace a makaranta tun lokacin shugaba Jonathan sun jajirce a kan bakan su. An dai yi nasarar gano kadan daga ciki da ma wasu dubannan dabam, sai dai sun ce har yanzu akwai jan aiki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Kungiyar BBOG a wata zanga-zanga

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel