Abin da ya sa Ahmed Musa ya rabu da matar sa

Abin da ya sa Ahmed Musa ya rabu da matar sa

– Babban Dan wasan gaban Najeriya Ahmed Musa ya saki matar sa

– Mataimakin Kyaftin din Najeriya ya nemi ya kara aure

– Matar sa tace sam ba za ta yarda ba ayi mata kishiya ba

Abin da ya sa Ahmed Musa ya rabu da matar sa

Dan wasan Ahmed Musa na Super Eagles

A baya NAIJ.com ta kawo labarin cewa Dan wasan gaban nan na Najeriya da kuma kungiyar Leicester City ta Ingila yayi wa matar sa duka wanda daga baya ya karyata ya kuma ce zai maka gidan jaridar da su ka fara masa wannan kazafi a kotu.

Yanzu haka majiyar mu ta bayyana mana babban dalilin da ya sa Dan wasan ya rabu da uwar ‘ya ‘yan sa. Ahmed Musa dai yayi niyyar kara mata, wanda mai dakin sa fa ta tubure tace sam ba za ta yarda ba duk da cewa addini bai hana ba.

KU KARANTA: Wani Dan Siyasa ya sha ature a Katsina

Abin da ya sa Ahmed Musa ya rabu da matar sa

Budurwar Dan wasa Ahmed Musa da zai aura

Abin ta kai har manya da iyaye su ka shigo cikin maganar domin a lallabi Jamila ta hakura da karin auren Mijin na ta amma abu ya faskara. Har Mahaifiyar Dan wasar ta je har Ingila domin ta shawo kan Sirikar ta amma fa tace sam ba za ta yarda ayi mata kishiya ba.

Hakan ta sa aka raba jiha tsakanin Ahmed din da Jamila uwar ‘ya ‘yan sa biyu bayan da ya tubure cewa sai ya kara aure ita ma ta cije.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Efa yayi nasara a Gasar Big Brother NAIJA

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel