Sarki Sanusi ya bayyana dalilin sa na goyon bayar ‘yar sa da ta mari namiji

Sarki Sanusi ya bayyana dalilin sa na goyon bayar ‘yar sa da ta mari namiji

- Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II ya bayyana dalilin da yasa ya goyi bayan ‘yar sa da ta mari wani namiji

- Ya ce ‘yar san a qyamar duk namijin da baya daraja mace

- Basaraken ya bukaci wadanda ke kai masa hari don ya fadi gaskiya da su kara kaimi kamar yadda yaransa dake tasowa zasu fi shi tsageranci, tsatsauran ra’ayi da kuma rashin tsoro

Sarkin Kano, Alhaji Sanusi II, ya tuna da yadda ya goyi bayan ‘yar sa, Shaheeda lokacin da ta mari wani namiji a lokacin da take makaranta.

NAIJ.com ta tattaro cewa Sanusi ya bayyana ‘yar sa, wacce ta wakilce shi a taron cikar yan matan Chibok shekaru uku da bata a Abuja a ranar Juma’a 14 ga watan Afrilu mutun ce na daban.

A cikin bidiyon basaraken ya gabatar da matashiyar yarinyar kafin ta gabatar da takarda a bakacin sa yace ba daidai bane ko wani namiji ya wulakanta mace.

Sarki Sanusi ya bayyana dalilin sa goyon bayar ‘yar sa da ta mari namiji

Sarki Sanusi ya bayyana dalilin sa goyon bayar ‘yar sa da ta mari namiji

Ya ce: “Koda dai b azan samu zuwa ba, na yanke shawarar tura ‘ya ta Shaheeda, ta wakilce ni maimakon da na.

KU KARANTA KUMA: Senata Abu Ibrahim ya sha da kyar bayan jama’ar mazaɓarsa sun kai masa hari (BIDIYO)

"Bara na fada maku wani abu game da wannan matashiyar wacce zata karanto jawabi na. Shaheeda ta kammala karatu daga makarantar African Leadership Academy dake Afrika ta Kudu sannan kuma ta kammala karatu daga jami’ar New York.

“Amman kafin ta tafi makarantar African Leadership Academy, lokacin da take aji uku na sakandare, na tuna da wani al’amari da yayi daidai da yau. Mahaifiyar ta ta zo gare ni tace: ya kamata kayi ma ‘yar ka magana sai na tambaye ta dalili?

“Ta ce: ‘Yar ka ta mari wani yaro a makaranta’. Kuma hakan sabon abu ne, don haka na kira Shaheeda sai nace: ‘Shaheeda, naji kin mari wani yaro a makaranta. Menene dalilin kin a yin haka?’

“Sai tace mun: ‘Ya mahaifina, wannan yaron bai daraja mata’. Don haka, sai na tambaye ta me take nufi da hakan. Sai ya zamana cewa wata rana, a cikin aji, yaron ya zo gare ta, sai yayi amfani da yatsar sa ya dungure mata kai zuwa baya, kuma hakan yake yi wa mata a aji.

“Bata ce komai ba a take sai ta jira washegari. Ta makara shiga aji, dukkan ajin ya cika, sai ta isa gare shi, ta mare shi sannan tace ‘bashin jiya da ka ci,” cewar sa a kan ‘yar sa Shaheeda.

A cewar sarkin, ‘yar sa ta kasance wacce bazata iya tsayawa namiji na wulakanta ta ba ta ko wani fanni da sunan aure.

KU KARANTA KUMA: Ni kai na ba ni da lafiya ina ga Buhari-Gwamna El-Rufai

Sanusi ya bukaci wadanda ke kai masa hari don ya fadi gaskiya da su kara kaimi kamar yadda yaransa dake tasowa zasu fi shi tsageranci, tsatsauran ra’ayi da kuma rashin tsoro.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A halin yanzu, a cikin wannan bidiyo da NAIJ.com ta kawo maku a kasa, Muhammadu Sanusi II ya soki shugabannin Najeriya kan talauci.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel