Muna fama da yunwa saboda mun kasance malalata – Sultan

Muna fama da yunwa saboda mun kasance malalata – Sultan

- Sultan na Sakkwato yace akwai yunwa a kasar saboda mutane na fama da lalaci

- Ya bayyana kasar Najeriya a matsayin mai cike da tarin albarkattun kasa

- Ya kuma yi kira ga yan arewa da su koma ga harkan noma domin shine abun alfaharin su a baya

- Sarkin musulmai ya bukaci al’umma da su yi zama na lafiya da sauran addinai

Sultan na Sakkwato, Muhammad Sa’ad Abubakar yace akwai yunwa a kasar saboda mutane na fama da lalaci.

“Shugaban kungiyar kungiyar Shura yayi magana game da yunwar dake kasar amma bari wayar mana da kai muna yunwa ne saboda mun kasance malalata,” cewar sa.

Ya mayar da martani ne ga kalaman shugaban kungiyar Shura na addinin musulunci, Ahmed Bello wadda ya bayyana cewa ana tsananin yunwa a kasar a gurin wani taro da akayi a Sakkwato.

Muna fama da yunwa saboda mun kasance malalata – Sultan

Sarkin Musulmai, Sa'ad Abubakar yace muna fama da yunwa saboda mun kasance malalata

Sultan ya bayyana cewa Najeriya na da kasa mai ni’ima sannan kuma idan ta yi amfani da shi yadda ya kamata zai kai kasar ga inganci amma saboda lalacin mutane.

Ya tuna da cewa harkan noma ya kasance abun alfaharin arewa a baya wanda akwai bukatar a dawo da hakan.

Basaraken ya bukaci yan Najeriya, musamman yan arewa da suyi amfani da damar shirin noma da gwamnatin jiha da na tarayya suke shiryawa don ci gaban yankin da kuma kasar baki daya.

Ya kuma yi kira ga haddin kan al’umma da kuma bukatar su yi zama na lafiya da sauran addinai.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da nan https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel