An gano fuskokin ‘Yan Kungiyar Boko Haram

An gano fuskokin ‘Yan Kungiyar Boko Haram

– An samu gane fuskokin wasu manyan ‘Yan Boko Haram

– Gidan VOA na Amurka ne dai da wannan kokari

– Hakan ya yiwu ne a dalilin bidiyon da ‘Yan ta’addan su ka saba fitarwa

An gano fuskokin ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Wasu ‘Yan Kungiyar Boko Haram

NAIJ.com na samun labarin cewa an gano fuskokin wasu daga cikin manyan ‘Yan kungiyar ta’addan Boko Haram. Gidan yada labarai na VOA watau Voice of America ne da wannan gagarumin kokari.

Gidan labaran na Amurka yayi wannan kokari ne a sanadiyar bidiyon da ‘yan ta’addar kan fitar a kai-a kai. Akwai wani Bidiyo da wani jagoran ‘Yan ta’addar wai shi Abu Umma ya dauka lokacin da ‘Yan kungiyar ke dajin Sambisa.

KU KARANTA: Bara ba Addinin mu bane Inji Sultan Sa'ad III

An gano fuskokin ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Wani Dan Kungiyar Boko Haram

Ana dai amfani da fuskokin da aka samu wajen gano ‘yan ta’addan. Haka kuma dai mutanen Yankin Adamawa da Yobe da Borno na amfani da hotunan domin gani ko ‘ya ‘yan su sun shiga cikin Kungiyar ‘Yan ta’addan.

Kwanaki mun kawo maku rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta maka wasu shugabannin ‘Yan Boko Haram har su 6 a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja. Ana zargin wadannan mutane da ta’addanci a Najeriya inda yanzu su hannun Hukuma.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Masu zanga-zangar BringBackOurGirls da Boko Haram su ka sace

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel