Ni kai na ba ni da lafiya ina ga Buhari-Gwamna El-Rufai

Ni kai na ba ni da lafiya ina ga Buhari-Gwamna El-Rufai

– Kwanaki Gwamnan Kaduna El-Rufai ya rubuta wasika ga shugaba Buhari

– Malam El-Rufai yace wasikar sa tayi amfani zuwa yanzu

– Gwamnan yace zai so shugaba ya tsaya takara zabe mai zuwa

Ni kai na ba ni da lafiya ina ga Buhari-Gwamna El-Rufai

Shugaba Buhari tare da Gwamna El-Rufai a Masallaci

Gwamnan Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai yace zai so shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya takara a zabe mai zuwa saboda tsanaki da ya kawo a harkar siyasar kasa. Malam El-Rufai yace ko da shugaban kasar ya tsufa zai so ya tsaya takara a 2019.

Malam El-Rufai ya bayyana wannan ne a wata hira da yayi da Gidan Channels TV. Gwamnan na Jihar Kaduna yake cewa shugaban kasar ya samu sauki amma tsufa ta kama sa don ko shi dan shekaru 56 yana fama da matsalar kwalastarol wanda yake shan magani, ina ga Buhari mai shekaru 70.

KU KARANTA: Ni da Buhari kamar da da uba ne-El-Rufai

Ni kai na ba ni da lafiya ina ga Buhari-Gwamna El-Rufai

Zan so Buhari ya kara takara-Gwamna El-Rufai

Kwanakin baya Gwamnan ya rubutawa shugaban kasar wasika yana ba sa shawara matakan da ya kamata ya dauka domin shawo kan matsalolin kasar. El-Rufai ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi maza yayi wasu gyara a mulkin sa wanda yace har an fara gyaran.

Wani mai ba tsohon shugaban kasa Jonathan Goodluck shawara a wancan lokaci watau Mista Reno Omokri yayi kaca-kaca da El-Rufa’i inda ya kira sa Munafuki. Reno Omokri yace bai dace Gwamna El-Rufa’i ya fallasa shugaba Buhari a bainar Jama’a ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hannun ka mai sanda daga wani dan APC

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel