Mota ta buge wasu mutane 2 har lahira

Mota ta buge wasu mutane 2 har lahira

- Hukumar NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 2 a babban titin mota na Legas zuwa Ibadan

- Hukumar NEMA ta ce, ta tuntubi hukumar FRSC don kawar da gawawakin daga hanyar

- Hukamar FRSC ta kira jama’a da su tuntubi ofishin hukumar FRSC na Sagamu da kuma na Mowe domin ganowa

Hukumar NEMA ta tabbatar da mutane 2 ne mota ya kashe a babban titin mota na Legas zuwa Ibadan.

A wata sanarwar kakakin hukumar, Mista Ibrahim Farinloye, a Legas a ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu yayin da yake fadan abin da mai daidaita ayyukan hukumar NEMA ta shiyyoyin kudu maso gabas, Alhaji Suleiman Yakubu, yana cewa zai iya kasance mota ne ya buge mutanen.

Kakakin hukumar ya ce: "An samu gawar wani matukin babur a gaban wani gidajen estate wato Majun City Estate, yayin da aka samu wani gawa kuma mai nisan kilomita 3 zuwa Mowe daga Ibadan.’’

Ya ce tuni suka tuntubi hukumar FRSC don kawar da gawawakin daga hanyar.

KU KARANTA KUMA: An gano fuskokin ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Hukamar na kiran mutane wadanda kila suna neman wani dan uwa ko makamanta aka da su tuntubi ofishin hukumar FRSC na Sagamu da kuma na Mowe domin ganowa.

NAIJ.COM ta ruwaito cewa kakakin ya shawarci yan babur da su nesanci yin amfani da baban titin mota, ya ce yin aka na da hadarin gaske.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun ke tukar matarsa a mota

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel