Tun da Buhari ya dawo daga Landan abubuwan Najeriya suka fara cakudewa - Inji Tanko Yakasai

Tun da Buhari ya dawo daga Landan abubuwan Najeriya suka fara cakudewa - Inji Tanko Yakasai

- Tanko Yakasai ya ce abubuwa sun sake daburcewa tun lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan.

- Yakasai ya yi bayani cedwa abubuwa suna tafiya yadda ya kamata a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

- Yakasai ya kara cewa idan har Buhari na da lafiyar da zai sake tsayawa takara karo na biyu yana masa fatan alkairi.

A wata hira da jaridar ‘The Sun’ ta yi da shaharren dan siyasar nan Tanko Yakasai, ya bayyana cewar tun lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga jinya ya karbi ragamar kasa daga hannun mataimakin sa abubuwa suka fara komawa gidan jiya.

Yakasai ya kara da cewar lokacin da shugaba Buhari yake birnin London abubuwa suna tafiya yadda ya kamata a karkashin jagorancin mataimakin sa, tsagerun Niger Delta sun daina fasa bututun iskar gas da kuma na fetur sannan ‘yan Nigeria suna samun wutar lantarki ta fiye da awanni takwas.

Yakasai ya ci gaba da cewar: “Abubuwa sunfi tafiya daidai lokacin da Osinbajo yake gudanar da mulki saboda ina samun wutar lantarki ta awanni sama da takwas, yanzu kuma da Buhari ya dawo wutar lantarki ta koma awanni 2 zuwa 3 a rana”.

KU KARANTA KUMA: Na baiwa Magu damar ci gaba da zama kan kujerarsa – Inji Buhari

Da aka juyo ta fannin tsadar rayuwa, Tanko Yakasai ya kara da cewa: “ Abunda bai kasheni a shekaru biyu da suka shudeba, bana tunanin zai kasheni a shekaru biyu masu zuwa. Wahala tayi yawa, Ina shan wahala kaima kana shan wahala, kowa na dandana kudar sa”.

NAIJ.COM ta tattaro cewa, Yakasai ya ce idan har Buhari ya ce yana da lafiyar da zai sake tsayawa takara karo na biyu, yana masa fatan alkairi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon ra'ayoyin mutane game da jita-jitar mutuwar shugaba Buhari a lokacin da yake hutu a Landon don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel