Idan Buhari ya matsa kan sai Magu ya zama shugaban EFCC, za a iya tsige shi – Inji Wani babban lauya

Idan Buhari ya matsa kan sai Magu ya zama shugaban EFCC, za a iya tsige shi – Inji Wani babban lauya

- Manyan lauyoyin kasar sun shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nemo wani amadadin mukaddashin hukumar EFCC Ibrahim Magu.

- Wani lauya ya ce za a iya tsige shugaba Buhari idon ya sake mika suna Magu ga ‘yan majalisa.

Manyan lauyoyin kasar nan suna ta tofa albarkacin bakin su game da batun sanotoci da su ka ki amincewa da Ibrahim Magu a matsayin ainihin shugaban hukumar cin hanci da rashawa, EFCC.

Babban lauyan nan Mike Ozekhome ya ce shugaba Buhari bai dace ya kara aika sunan Magu ba don kuwa an yi wannan ba sau daya ba kenan.

Ozekome ya ce sai dai shugaban kasa ya nemo wani don kuwa ba Ibrahim Magu kadai ne kai iya shugabancin hukumar ba. Inji NAIJ.COM.

Idan Buhari ya matsa kan sai Magu ya zama shugaban EFCC, za a iya tsige shi – Inji Wani babban lauya

Shugaba Muhammadu Buhari

Shi kuwa babban lauya JB Daudu, cewa ya yi bai halatta Magu ya ci gaba da zama a ofishin hukumar ba. Daudu ya kara da cewa kai har ana iya tsige Buhari idan ya kara aikawa sanatoci sunan Ibrahim Magu. Babban lauyan ya ce kwanakin Magu sun kawo karshe a matsayin mukaddashin hukumar.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu Shugaba Buhari bai fitowa daga gidan sa ba a cikin Villa

Sai dai wasu suna ganin akwai lauje cikin nadi a maganar. Wasu ma dai suna ganin cewa mafi yawan sanatocin ba za su rasa kashi a duwawun su ba, don haka su ke gudun Ibrahim Magu. Shi dai Ibrahim Magu ya ce ko ta yaya dai sai yaki sata a kasar.

Majalisar Dattawa dai ta ki amincewa ta tantance Magu ne bisa wasu zargi da hukumar DSS ta yi a kansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wani mutumi da yayi barazanar yin sata idan abubuwa basu daidaita ba:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel