Madalla: Farashin kaya sun fara sauki a Najeriya

Madalla: Farashin kaya sun fara sauki a Najeriya

– A halin yanzu farashin kaya sun fara sauki a Najeriya

– Babu mamaki yunkurin da Naira tayi a baya ne sababi

– Alkaluma su na cigaba da bayyana cewa tattalin Najeriya na farfadowa

Madalla: Farashin kaya sun fara sauki a Najeriya

kaya sun fara sauki a Najeriya

Najeriya mai fama da durkushewar tattalin arziki tun bayan ragargajewar farashin man fetur na murmurewa bayan da alkaluma suka nuna cewa tsadar kaya na kara sauki a cikin kasar a wani nazari da aka fitar na kwanan nan.

NAIJ.com na da labari daga Hukumar tara bincike da alkaluman kasa watau NBS cewa farashin kaya sun fara yin kasa a Najeriya. Farashin kaya sun sauka kasa da kashi 0.52% watau cikin kashi dari.

KU KARANTA: Bara ba Addini musulunci ba ne Inji Sarkin Musulmi

Madalla: Farashin kaya sun fara sauki a Najeriya

Wata kasuwa a Garin Legas

Alkaluman yanzu dai sun nuna cewa tsadar kaya yana kan kashi 17.26% wanda ba karamin cigaba aka samu daga watan baya ba da alkaluman ke kan 17.78%. Abubuwa suna dai kara mikewa har ta kai kwanaki darajar dala ta daga kwarai.

Kuna da labari kuma jiimilar kudin kasar watau GDP yana ta kara yawa ne kamar yadda nazari ya nuna. Bugu da kari kudin kasar waje na kasar shi ma yana kara yawa a wannan lokaci da ake ciki.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kaya a kasuwanni

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel