Yadda aka yi kokari a kashe shugaban kasa a baya

Yadda aka yi kokari a kashe shugaban kasa a baya

– Wani tsohon Soja ya bayyana yadda aka yi kokari a kashe Obasanjo

– Kanal Oloruntoba ya bayyana cewa an yi kokarin ganin bayan tsohon shugaba Obasanjo

– Oloruntoba yana cikin wadanda suka tsaya tsayin-daka game da zaben Abiola

Yadda aka yi kokari a kashe shugaban kasa a baya

Shugaban kasa Buhari da Obasanjo

Wani tsohon Kanal na Soja ya bayyana irin yadda aka yi yunkurin kashe Olusegun Obasanjo a shekarar 1998. Kanal Olusegun Oloruntoba yana cikin wadanda ba su yarda da soke zaben Abiola ba har ta kai aka jefa sa gidan yari.

Takwaran tsohon shugaban kasar Kanal Olusegun Oloruntoba yace an yi kokarin kashe Obasanjo da wasu Sojoji da aka saki a 1998. Kanal din mai ritaya yace an yi yunkurin tada jirgin saman ne ya watse kowa ya mutu.

KU KARANTA: Wani jigo a gwamnatin Obasanjo ya cika

Yadda aka yi kokari a kashe shugaban kasa a baya

Yadda aka yi kokarin kashe Obasanjo

NAIJ.com na samun wannan labari ne ta wata hira da aka yi da tsohon Sojan a wata Jarida. An dai daure Janar Obasanjo da wasu manyan Sojoji a lokacin Marigayi Janar Sani Abacha, daga baya kuma Obasanjo ya zama shugaban kasa.

A wannan makon aka yi kokari kashe wani Sanatan Jihar Kogi mai suna Dino Melaye. Sai dai har yanzu Jami’an tsaro ba su yi magana ba game da lamarin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sojojin saman Najeriya a bakin aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel