An jefi wani Sanata da duwatsu a garin sa

An jefi wani Sanata da duwatsu a garin sa

– Muna da labarin cewa Sanata mai wakiltar Kudancin Katsina ya sha duwatsu a gida

– Sanata Abu Ibrahim dai ya sha da kyar ne a jiya

– Gwamna Masari ya kaddamar da kasuwa a Garin Funtuwa

An jefi wani Sanata da duwatsu a garin sa

Jama’a sun jefi Sanata Abu Ibrahim a Funtua

NAIJ.com na da labari cewa Sanata mai wakiltar Kudancin Jihar Katsina watau Abu Ibrahim ya sha ruwan duwatsu da kasa yayin da ya kai ziyara mazabar sa ta Garin Funtua. Sanatoci da dama dai na fuskantar wannan barazana musamman a Arewa.

Wannan abu ya faru ne a jiya lokacin da Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya fara shirin gina wata katafariyar kasuwa a Yankin. Wani da abin ya faru a gaban sa yace Sanatan ya sha jifa da duwatsu da kasa.

KU KARANTA: Ana shirin maido wani Sanata gida

An jefi wani Sanata da duwatsu a garin sa

An jefi wani Sanata a garin sa

Majiyar mu ta nuna mana cewa da kyar Sanatan ya sha, inda wani yace mana ma kadan-ke-nan sai zuwa shekarar 2019 da za ayi zabe. Wasu ‘yan mazabar sun koka sun ce Sanatan yayi watsi da su gaba daya.

Sanata Dino Melaye mai wakiltar Jihar Kogi ya bayyana cewa an yi kokarin ganin bayan rayuwar sa a jiya Asabar. Sai dai kuma har yanzu Jami’an tsaro sun gagara cewa uffan game da lamarin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Dan APC ya gargadi Jam'iyyar ta su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel