Ruwan sama yayi gyara a Jihar Kano

Ruwan sama yayi gyara a Jihar Kano

– A Jihar Kano ruwan sama ya rusa gidaje da dama

– Abin ya kai har dai an rasa rai guda

– Wannan karo dai an shiga daminar da gyara

Ruwan sama yayi gyara a Jihar Kano

Yadda ruwan sama yayi gyara a wata kasa

A cikin Jihar Kano wannan karo dai an shigo daminar da gyara inda gidaje kusan 1000 su ka rugurguje a Garin karamar Hukumar Kura kamar yadda NAIJ.com ke samun labari a halin yanzu.

Wannan abu ya faru ne dai tun a tsakiyar wancan makon kamar yadda mu ke jin labari. An dai yi ruwa ne tare da mugun tsawa wanda ya debe saman kwanon gidaje da dama a Garuruwan Zagazagi, Tofa, Iyatawa da sauran su.

KU KARANTA: Ra'ayi: Sarkin Kano adali ne ko kuwa?

Ruwan sama yayi gyara a Jihar Kano

Gwamnan Jihar Kano tare da Sarkin Kano

Shugabannin karamar Hukumar yankunan sun zagaya domin jajantawa wadanda abin ya shafa. Sai dai har yanzu Gwamnatin Jihar ba tace komai ba tukun game da maganar. An dai yi kira da Gwamna ya kawo dauki. Har an yi rashin mutum guda a hadarin.

NAIJ.com ta kawo maku rahoto cewa farashin kaya sun fara yin kasa a Najeriya. Farashin kaya sun sauka kasa da kashi 0.52% watau cikin kashi dari. Wannan da na da alaka da tashin da Naira tayi kwanalo.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana tsakiyar hutun 'Easter' a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel