Gwamnati za ta gina wata babban kasuwar zamani a Funtua

Gwamnati za ta gina wata babban kasuwar zamani a Funtua

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya kaddamar da gina wata sabuwar kasuwar zamani a Funtua.

- Gwamnan ya ce fiye da shagunoni 500 za a gina a kasuwar don inganta kasuwancin da kuma zuba jari a cikin kasuwar.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a ranar Asabar, 15 ga watan afrilu ya kaddamar da gina wata sabuwar kasuwar zamani a Funtua wanda zai bukaci miliyan 800 da kuma tashar mota don bunkasa tattalin arziki da aikace-aikace a garin Funtua.

Da yake jawabi a lokacin kaddamarwar, gwamna Bello Masari ya ce fiye da shagunoni 500 za a gina a kasuwar don inganta kasuwancin da kuma zuba jari a cikin kasuwar.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, gwamna Bello Masari ya shawarci 'yan kasuwa cewa su yi amfani da damar da gwamnati ya bayar, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta farfado da hanyar jirgin kasa da kuma wasu kamfanonin ayyukan gona don bunkasa tattalin arzikin jihar.

Za a gina wata babban kasuwar zamani a Funtua

Gwamna Bello Masari ta jihar Katsina

KU KARANTA KUMA: To fa! Wani mataimakin Gwamna Masari ya aje aikin sa

Da yake jawabi a wurin kaddamarwar, kwamishinan ayyuka a jihar, Alhaji Tasi'u Dandagoro, ya ce gwamnati ta sallami 'yan kwangila don fara aikin dagan-dagan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali yadda mutanen Daura a jihar Katsina ke murnar dawowar shugaba Buhari daga Landan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel