Ka yi koyi da marigayi Ado Bayero wajen dattaku -
 Inji Yari

Ka yi koyi da marigayi Ado Bayero wajen dattaku - Inji Yari

- Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya kuma kai hari ga sarkin Kano, Sanusi Lamido

- Gwamnan ya zargi Sanusi da munafurci, yace baya nuna kula game da talaucin da mutenan sa ke fama da shi

- Ya kuma shawarci Sarki Sanusi da yayi aikata abunda yake wa’azi a kai maimakon ya dunga jifar sauran mutane da zargi

Gwamnan jihar Zamfara AbdulAzeez Yari ya yi kira ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ya yi koyi da yadda tsohon Sarkin Kano Ado Bayero ya gudanar da mulkin Kano a lokacin ya na raye.

Yari ya fadi hakan ne a martanin da ya maida wa sarkin Kano Sanusi kan maganar da yayi game da cutar Sankarau.

AbdulAzeez Yari ya yi kira ga mutane da su daina sabon Allah sannan a yawaita neman gafaransa ko ya tausaya mana ya kawo karshen cutar Sankarau da ake fama dashi wanda ba’a taba yin irin sa ba.

Ka yi koyi da marigayi Ado Bayero wajen dattaku -
 Inji Yari

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari

Jihar Zamfara ne ta fi yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar bullowar cutar zuwa yanzu.

Fadin haka ke da wuya Sarki Sanusi a jawabin sa da yayi a Kaduna ya ce abinda gwamnan ya fadi ba karantarwan musulunci bane. Ya yi kira ga gwamnan da ya nema wa mutanen jihar sa magani maimakon hada cutar da ikon Allah da ya ke yi.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigo a gwamnatin Obasanjo ya rasu

Dalilin haka ne ya sa gwamna Yari ya baiwa Sarki Sanusi amsa akan abin da ya ke kiransa da yayi.

NAIJ.com ta tattaro takardar wanda mai ba gwamnan shawara akan wayar da kan mutane da yada labarai Ibrahim Dosara ya sanya wa hannu Yari ya ce maimakon Sarki Sanusi ya kirkiro hanyoyin da zai taimakawa mutanen kasar sa da irin dinbim waye wa da yake ikirarin ya na da shi ya kan bige ne da hawa manyan motoci kawai bayan mutanensa na bukatar taimako.

Ya ce da ma can Marigayi Sheikh Ja’afar ya taba yin wa’azi ta musamman akan Sarki Sanusi inda ya ce “Sarki Sanusi makiyin addinin Musulunci ne.

“Maimakon Sarki Sanusi ya wanke kansa akan zargin da ake masa na yadda ya wawushe bilyoyin kudaden masarautar Kano, ya bige da kullum sai dai yace wannan gwamnan ya yi kaza wancan yayi kaza.”

Daga karshe ya roki Sarki Sanusi da ya yi koyi da tsohon Sarki Marigayi Ado Bayero wajen dattaku a matsayinsa na Sarkin babban Masarauta kamar Kano.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/ Da nan https://twitter.com/naijcomhausa

Wani jami'in APC ya fadi dalilin da zai sa a kayar da jam'iyyar sa a 2019:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel