Ana shirin yi wa sanata kiranye a Kaduna

Ana shirin yi wa sanata kiranye a Kaduna

- Wata kungiya a jihar Kaduna na faman karbar sa-hannun jama'ar yankin arewacin jihar domin yi wa sanatan da ke wakiltar su kiranye

- Sanata Sulaiman Hunkuyi dai na wakiltar arewacin jihar ta Kaduna a majalisar dattawan kasar

- wasu na bangaren sanata Hunkuyi sun musanta zargin

- Gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa dangane da batun, a inda ta ce tana tare da sanata Hunkuyi

Wata kungiya a jihar Kaduna na faman karbar sa-hannun jama'ar yankin arewacin jihar domin yi wa sanatan da ke wakiltar su kiranye bisa gazawa.

Sanata Sulaiman Hunkuyi dai na wakiltar arewacin jihar ta Kaduna a majalisar dattawan kasar.

Kungiyar ta masu son yi wa sanatan kiranye ta ce kawo yanzu ta samu nasarar tattara sa-hannun mutane fiye da dubu 10.

Ana shirin yi wa sanata kiranye a Kaduna

'Yan yankin sanatan sun ce wakilin nasu ya gaza wakiltarsu

Ana dai zargin sanata Hunkuyi da kasawa a majalisar, a inda masu son yi masa kiranyen suka ce bai taba kai kuduri zauren ba.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigo a gwamnatin Obasanjo ya rasu

Sai dai kuma wasu na bangaren sanata Hunkuyi sun musanta zargin, a inda suke fadin cewa masu hamayya da sanatan ne suke kitsa shirin yi masa kiranye.

NAIJ.com ta rahoto cewa tuni gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa dangane da batun, a inda ta ce tana tare da sanata Hunkuyi kuma abun da kungiyar ke zargin sanatan babu kanshin gaskiya a ciki.

Wasu dai na ganin idan batun yi wa sanatan kiranye ya yi nasara to zai bude wani sabon babin masu zabe su rinka yi wa wakilan nasu kiranye idan ba sa yin abun da suke so.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da nan https://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan siyasan Najeriya ne baida ra'ayin cin hanci? Kalli ra'ayin jama'a a cikin wannan bidiyo:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel