Ra'ayi: Sarkin Kano Sanusi II adali ne

Ra'ayi: Sarkin Kano Sanusi II adali ne

- Wani bawan Allah mai suna Mujtaba Tela ya fadi ra'ayinsa game da masu zagin sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido II

- Ya bayyana sarkin a matsayin adalin shugaba domin irin tallafi da ya basa a rayuwa

Wani bawan Allah mai suna Mujtaba Tela ya fadi ra'ayinsa game da masu zagin sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido II. Inda bayyana sarkin a matsayin adalin shugaba domin irin tallafi da ya basa a rayuwa.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigo a gwamnatin Obasanjo ya rasu

Mujtaba ya ce: "Ni ba zan gushe ina tausayawa masu zagin wannan adalin Sarki ba har sai sun tuba sun nemi gafarar Ubangiji.

"Ni Mujtaba Tela ne, iyayena sun mutu sun bar ni da marayu uku, na yi aure kuma nauyi da wahalhalu suka karu tun ina samar da bukatu har ta kai bana iya biyan kudin hayar gidan da muke dalilin haka na yi rance wajen wani me kawo min dinki na biya amma har aka kusan shafe shekara ban biya ba. Hakan ce tasa aka kaini gaban shari'a daga nan kuma aka tura ni gidan wakafi.

Ra'ayi: Sarki Kano Sanusi II adali ne

Wani bawan Allah yace Sarki Kano Sanusi II adali ne

"Shekarata uku a kulle matata da take kula da kannena itama mahaifinta ya rasu don haka ta ce to, ita ta yi iya nata su je su nemi temako wajen mutane kuma.

"Yaran nan dukka ba wacce ta kai shekaru sha 14. Wani ya ba su shawara su je wajen Sarki Sanusi, ba tare da sun sha wahala ba suka je suka sanar da shi halin da muke ciki.

"A washe garin ranar Sarki ya yi hawa ya shiga gidan firsina ya nemi a tattara masa dukka wadanda ake bi bashi da masu kananan laifuffuka wanda masu shari'a sukai fushi da su bai ware dan Kadiriyya ko Tijjaniya ko Izala ba a'ah dukkanmu mutum sama da hamsin ya hada ya biya mana bashin da ke kanmu ya fansomu daga cikin ukubar zaman gidan yari.

Ku dubi yawanmu a durkushe a gabansa, dukkanmu mun shafe lokaci cikin kangin wahala, in ba adali ba mai tausayin talakawansa Waye zai yi wannan temako, Allah ya sakawa Sarki da alheri.

Ra'ayi: Sarki Kano Sanusi II adali ne

Mujtaba yace tana tausayawa masu zagin sarki Sanusi

"Irin wannan namijin kokari bai tsaya anan ba har sai da ya tallafa man da abinda zamu ja jari. Sannan yayi mana wa'azi ya yi kira gare mu da mu kiyaye dokokin Allah da hakkokin jama'a idan mun fita zuwa gidajenmu kar mu sake aikata laifin da zai kaimu firsina.

"Ina rokon wadanda basu fahimci Sarkin nan ba da 'yan abi yarima asha kid'i don Allah kar su yiwa Allah bore bisa neman tozarta abinda ya zab'a mana da kansa. Kar mu zamo masu butulci wanda bama godewa ni'imar da Allah yai mana sai bayan ta gushe.

"An sha jifan marigayi Sarkin Kano Ado, An sha yi masa rashin kunya irinta siyasa lokacin Rimi, an sha yi masa sharri da mata, amma ga shi yau babu shi kuma ana yabonsa ana ganin shi ya iya mulki. Me yasa ba zamu ga tarin ni'imomin da Allah ya yiwa mutum ba sai bayan babu shi?

"In zaka tambayi dukka wadanda suke cewa Sarki ya cika magana cewa maganar da yake fada gaskiya ce ko karya ce to, lallai zasu gaya maka duk abinda yake fada gaskiya ne.

"Gazawar Sarkin Kano Sanusi a wajen wasu bai wuce saukin kansa ba, wai baya mulki da izza da girman kai da isa, yana mu'amala da kowa da kowa. To, in shugaba bai saurari talakawansa ya ji koke-kokensu ba, ta ina zai taimakesu.

"Gazawarsa da yake fyede gaskiya ya bawa shugabanni shawara suyi abinda zai amfanar da talakawansu. Shi yasa karnukan siyasa suke tai masa haushi.

"Gazawarsa da yace Malamai su farfado da mutuncin aure kamar yadda yake a musulunci su jaddada abubuwan da za su kare mutuncin addinin Allah. Shi ya sa aka fito da wata tsohuwar hira ta Mallam Jaafar ake yadawa don a zubar masa da kima. Wannan na nunin cewa wasu mabiya kiyayya da riko da kuma gaba shi ne abinda suka sanya a gaba ba addini da kishin al'umma ba.

"Sarkin nan masani ne a kowanne bangare na ilimin zamani da na ilimin addini ya doke da yawan malaman da ake fifita darajarsu don wallahi ba matsayin da muke basu bane zai cece su matsayin da Allah yake bawa mutum shi ne zai cece shi.

"Ina kira gareku ya ku 'yan uwa musulmi mu yiwa juna afuwa mu hadu waje daya mu dinke domin wallahi barakar da ke taskaninmu ce ta hanamu juya duniya. Mu cire hassada da gaba da baqar siyasa wacce zata kaimu ga halaka. Mu girmama shugabannin da suke tausaya mana kar mu zamto marasa tarbiyya masu zage-zage."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon rikicin da ya afku a Ile-Ife tsakanin Yarbawa da Hausawa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel