Tsakanina da Buhari kamar da ne da Uba – Inji El-Rufai

Tsakanina da Buhari kamar da ne da Uba – Inji El-Rufai

- El-Rufai yace bai ta ba samun matsala da Buhari ba kamar yadda ayi ta yadawa a kafafen yada labarai

- Ya ce abunda baya ziyartar Buhari akai akai yanzu shine domin ganin cewa shugaban kasan na bukatar hutu

- El-Rufai yace babu wanda ya Isa ya hana shi shiga fadar shugaban kasa

Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya sanar wa manema labarai a fadar Shugaban kasa a ranar Juma’a cewa Buhari Ubane a garesa kuma ya na matukar Alfahari da hakan.

Gwamnan ya kara da cewa bai ta ba samun matsala da shugaban kasa MuhammaduBuhari ba kamar yadda ayi ta yadawa a kafafen yada labarai

Ya ce dalilin da yasa baya ziyartar Buhari akai akai yanzu shine domin ganin cewa shugaban kasan na bukatar hutu.

Tsakanina da Buhari kamar da ne da Uba – Inji El-Rufai

Gwamna El-Rufai tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari

“Shugaban kasa yana bukatan lokaci sosai domin samun hutu saboda ganawa da mutane ya na daga cikin abubuwan dake gajiyar da shugaba.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigo a gwamnatin Obasanjo ya

“Ni gwamna ne kuma a duk lokacin da na gana da mutane a kalla 10 a rana na kan gaji. Ba yawan takardun da zaka sa ma hannu bane ke gajiyar da shugaba, mutanen da ke shiga da fita su ne ke gajiyar da kai.

“Bana so in takura ma shugaban kasa wajen zuwa kullum amma muna ganawa da shi."

Da farko NAIJ.com ta tattaro cewa, El-Rufai yace babu wanda ya Isa ya hana shi shiga fadar shugaban kasa.

El Rufai yace: “Babu wanda ya ta ba hani shiga fadar shugaban kasa kuma babu wanda ya isa ya hani zuwa ko shiga.

“A matsayina na gwamna bani da shamaki da fadar shugaban kasa, babu wanda zai bincike ni, kawai na ga ya kamata ne in dan daga kafa domin ya samu hutun da yake bukata.”

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani mutumi da ya yi barazanan yin sata idan abubuwa basu daidaita ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel