‘Naji dadi Buhari na cikin koshin lafiya, zai iya jagorantar Najeriya’- Sanata Abu Ibrahim

‘Naji dadi Buhari na cikin koshin lafiya, zai iya jagorantar Najeriya’- Sanata Abu Ibrahim

- Sanata Abu Ibrahim na Katsina ta kudu yace shugaban kasa Buhari na cikin koshin lafiya

- Bayan ya kai ziyara ga shugaban kasar a Aso Rock, yace yana da tabbacin Buhari zai iya jagorantar kasar

- Ya bi sahun wasu masu ruwa da tsaki a jihar Katsina wadanda suka hada da gwamnan jihar gurin jinjina biyayyar su ga shugaban kasar

Sanata Abu Ibrahim dake wakiltan Katsina ta kudu, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin koshin lafiya sannan kuma yana da kwarin da zai iya shugabantar kasar.

Bayan ya kai ziyara ga shugaban kasa a fadar Villa dake Abuja a ranar Juma’a 14 ga watan Afrilu, ya fada ma manema labarai na fadar shugaban kasa: “Naji dadi sosai, ina da tabbacin cewa shi (Buhari) na cikin koshin lafiya a yanzu.”

Ya kuma tunda da wani ziyara ga shugaban kasar a ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu lokacin da ya bi wasu masu ruwa da tsaki daga jihar Katsina wadanda suka hada da gwamnan jihar, Alhaji Aminu Masari da kuma sarakunan gargajiya gurin jinjina biyayyarsu ga shugaban kasar.

‘Naji dadi Buhari na cikin koshin lafiya, zai iya jagorantar Najeriya’- Sanata Abu Ibrahim

Shugaban kasa Buhari ya halarci sallar Juma'a a ranar 14 ga watan Afrilu

Sanata Abu yace: “Ziyaran ranar Alhamis da aka kai ga shugaban kasa ya kasance tamkar al’amarin yan’uwa. Mahaifinmu kuma babban yayanmu (shugaban kasa) yayi rashin lafiya sannan kuma ba sabon abu bane don yan uwansa sun zo gaishe da shi bayan ya dawo, don haka al’amarin yan’uwantaka ne.

KU KARANTA KUMA: JIYA BA YAU BA: Ku kalli shugaba Buhari tare da Kanal Hamid Ali a lokacin gwamnatin soja (HOTO)

“Don haka mun gaishe da shi sannan kuma munyi farin ciki da cewan yana cikin koshin lafiya sannan kuma ya dawo kuma ina da tabbacin cewa yana da lafiyan da zai ci gaba da shugabanci.

“Mun dada jaddada biyayyarmu gare shi sannan kuma shima ya gode mana kan goyon bayan mu da kuma shawarwarin da muke ba shi daga lokaci zuwa lokaci.”

Sakon sanatan ya zo ne a kan lokaci yayinda aka daukaka sabon damuwa kan lafiyar Buhari.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa shugaban kasar bai samu halartan zaman majalisa na sati-sati ba wanda aka gudanar a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu a fadar shugaban kasa, Abuja. Mataimakin sa Osinbajo ne yam aye gurbin sa.

Wannan shine karo na farko da Buhari bai samu halartan zaman majalisa bat un ranar 10 ga watan Maris lokacin da ya dawo daga Landan inda yayi dogon hutu yana ganin likita.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da nan https://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com tayi hira da yan Najeriya game da lafiyar shugaban kasa Buhari amma ga abunda suka ce:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel