Dakuku Peterside yace Wike na janyo musu abin kunya

Dakuku Peterside yace Wike na janyo musu abin kunya

- Tsohon dan takaran gwamnan jihar Ribas yace Nyesom Wike ya samu tabin hankali

- Peterside yace Wike na jawo abin kunya ga kujerar gwamnan jihar Ribas

Wani jigon APC a jihar RIbas, Dakta Dakuku Peterside tace ayi dubi zuwa ga hankalin gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike bayan yayi ikiraarin cewa kudin da aka gano a jihar Legas ta jihar Ribas ne.

Wike yace kudin da aka samu wajen siyar da injin iskar gas ne lokacin gwamnatin magabacinsa, Chibuike Rotimi Amaechi.

Peterside, wanda tsohon dan takaran gwamna ne a jihar Ribas kuma dirakta janar na hukumar tabbatar da tsaron man fetur na ruwa wato Nigeria Maritime Administration and Safety Agency (NIMASA), yace Wike mahaukaci ne.

Wike ya samu tabuwan hankali, ya kamata a duba shi – Dakuku Peterside

Wike ya samu tabuwan hankali, ya kamata a duba shi – Dakuku Peterside

“Ba da dadewa ba, Wike cikin mayensa yace ya bayar da kwangilan aiki can jihar Benuwe. Haka zalika kuma ya tuhumci Sifeto Janar na yan sanda cewa yana kokarin hallakashi ta hanyar kwamishanan jihar Ribas.

“Muna tunanin wasa kawai yakeyi. Amma abin mamaki shine kokarin jinginawa magabacinshi kudin da aka gano.”

KU KARANTA: Kalli yadda masu bauta a coci ke cin karansu ba babbaka

“Lokuta da dama, Wike na kawo abin kunya ga kujeran da yake zauna da kuma mutan jihar Ribas wadanda aka sani da hankali, ilimi, da kyawawan dabi’u.”

Peterside yace ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya musanta maganar cewa shine mamallakin gidan da aka gano kudi kuma ya kalubalanci gwamnatin jihar Ribas ta bada hujja akan hakan.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel