Bani da matsala da Dogara, kani na ne – Nasir El-Rufai

Bani da matsala da Dogara, kani na ne – Nasir El-Rufai

-El-Rufai yace kakakin majalisa Yakubu Dogara na ganin girman sa

- Kana kuma yace kanin sa ne basuda wata sa’insa tsakaninsu

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yace bashi da matsala da Yakubu Dogara, kakakin majalisan wakilai, wand ya siffanta a matsayin dan kaninsa.

Wadannan jigogin jam’iyyar APC sun kasance cikin sa’insa makon da ya gabata tun lokacin da El-Rufai ya kalubalanci majalisan wakilai ta wallafa kasafin kudinta.

Dogara ya kalubalanci gwamnoni su wallafa kudin tsaron da aka basu da kuma na kananan hukumomi.

Bani da matsala da Dogara, kani na ne – Nasir El-Rufai

Bani da matsala da Dogara, kani na ne – Nasir El-Rufai

Kwanaki 3 bayan wannan takaddama, El-Rufai ya wallafa kudinsa kuma Dogara shi ma ya wallafa nasa. Wannan abu ya cigaba har ranan Alhamis.

Yayinda yake magana da manema labaran fadar shugaban kasa, El-Rufai yace bashi wani matsala da kakakin majalisan wakilan Najeriya.

KU KARANTA: Anyi asaran dukiyoyi a gobaran jihar Sokoto

Yace kowani dan Najeriya na da hakkin fadawa majalisan dokoki ta wallafa kasafin kudinta kuma shi yayi hakan ne saboda soyayyar kasa.

“Bani da matsala da kakakin, kanina ne. ina ganin girmanshi kuma yana ganin girma na,”

“Da yafi ma majalisan dokoki ta wallafa kasafin kudinta saboda jita-jitan da ake yadawa akan kudin albashinsu wanda ban yarda da shi ba.”

“Ina tunanin hanya mafi kwarai da zasuyi watsi da jita-jitan shine su wallafa kasafin kudi amma wasu suna ganin cewa nayi laifi domin kira ga gaskiya.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel