Jami’in tsaron Najeriya da dan fashi sun rasa rayukansu a musayar wuta

Jami’in tsaron Najeriya da dan fashi sun rasa rayukansu a musayar wuta

- Wani jami’in tsaro na hukumar tsaro da wanzar da zaman lafiya ta ‘Civil Defence’ dake aiki da hukumar a jihar Bayelsa ya rasa ransa tare da wani ɗan fashi da makami a wata musayar wuta da akayi.

- Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito cewa musayar wutar ta farune akan titin Kolo Creek a ƙaramar hukumar Ogbia dake jihar

Kwamandan hukumar ta NSCDC a jihar Desmond Agu ya tabbatar da faruwar hakan, inda yacae wasu mutane sun kai harin kwantan ɓauna kan motar sintiri ta jami’an mu, wanda hakan ya janyo mutuwar jami’i ɗaya.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Ya kuma yabada ƙoƙarin jami’an kan yadda suka mai da martani, har suka ci ƙarfin ƴan fashin inda hakan ya jnyo mutuwar mutum guda daga cikinsu,tare da samo bindigar ɗan fashin da yarasa ransa a musayar wutar.

Mr Agu yace rundunar ta miƙa bindigar da kuma gawar ɗan fashin ga rundunar ƴansanda ta jihar.

Jami’in tsaron Najeriya da dan fashi sun rasa rayukansu a musayar wuta

Jami’in tsaron Najeriya da dan fashi sun rasa rayukansu a musayar wuta

A tabakin wani wanda yaganewa idonsa abinda yafaru wanda ya nemi a sakaya sunansa yace ƴan fashin sunyiwa jami’an kwanton ɓauna bayan da suka suka kai hari kan shingen binciken jami’an tsaro.

KU KARANTA:

“Bayan sun tsere daga wurin da suka kai harin sai suka hangi motar sintiri ta jami’an na ‘Civil Defence’ inda suka ɓuya cikin daji.

“Lokacin da motar tazo sai suka buɗe wuta akan motar suka kashe jami’i ɗaya.

“Amma jami’an sun maida martani kan ƴan fashin suka kashe ɗaya daga yayin da ragowar suka ranta a nakare,” yace.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai jirgin yakin jami'an tsaron Najeriya ne

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel