Babu wanda ya hanani ganin Buhari – Inji gwamna El-Rufai

Babu wanda ya hanani ganin Buhari – Inji gwamna El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, malam Nasiru El-Rufa'i ya karya jita-jita da ke yawo a yanar gizo cewa an dakartar da shi daga zuwa fadar shugaban kasa

- Gwamna ya ce babu wanda zai iya dakatar da shi daga ziyartar fadar shugaban kasa

Gwamnan jihar Kaduna, malam Nasiru El-Rufai ya babu wanda ya taba dakatar da shi daga zuwa fadar shugaban kasa da ke Abuja.

NAIJ.COM ta tattaro cewa, gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan sallah juma’a tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a masallacin fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja, a ranar Juma'a, 14 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari ya kori shugabannin hukumomin CPC, PENCOM da wasu fiye da 25

Rahotanni a yanar gizo na nuna cewa an dakartar da El-Rufai daga fadar shugaban kasa da bisa zargin bayyana wata wasika da ya rubuta wa shugaba Buhari a watan Satumba 22, 2016.

Babu wanda ya hanani ganin Buhari – Inji gwamna El-Rufai

Shugaba Buhari da gwamna El-Rufai na gaisawa bayan sallah juma'a a masallacin fadar shugaban kasa

El-Rufai, duk da haka, ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa da cewa bai daina zuwa Aso Rock ba, kuma a cewarsa babu wanda zai iya dakatar da shi daga ziyartar fadar shugaban kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon taron farfado da tattalin arziki na 2017 wanda aka sani da KADINVEST a Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel